Matashiya ta bayyana kanta a matsayin wadda ta yi kutse a shafin Hisbah

0
97
Matashiya ta bayyana kanta a matsayin wadda ta yi kutse a shafin Hisbah

Matashiya ta bayyana kanta a matsayin wadda ta yi kutse a shafin Hisbah

Wata matashiya ta bayyana kanta a matsayin wadda ta yi kutse a shafin Facebook na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da yadda aka yi shafin hukumar kutse, inda ya roƙi jama’a su taimaka wajen dawo da shafin.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta tuntuɓi kamfanin Meta, don taimaka musu kan yadda za su dawo da shafin daga hannun waɗanda suka yi musu kutse.

Shugaban Sashen Kimiyya da Fasaha na Hisbah, Sani Zailani, ya bayyana cewa an taɓa yi wa asusun kutse a baya kuma Meta ta yi alƙawarin magance matsalar cikin sa’o’i 48.

Sai dai, bayan sa’o’i 72 da yin kutsen, wata mai amfani da Facebook mai suna Mariam Oyiza Aliyu, ta ce ita ce ta yi wa shafin hukumar kutse.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Hisbah ta haramta wa ɗaliban Kano bikin kammala karatu

Oyiza, wadda ta ke da mabiyan 13,000 a Facebook, ta bayyana kanta a matsayin mai kare haƙƙin ɗan Adam, tsohuwar Musulma kuma mai goyon bayan mata.

Bayanan da ta ɗora a shafinta, sun nuna cewa ita ‘yar asalin garin Okene ce, da ke Jihar Kogi, amma bayananta sun nuna yanzu haka tana zaune a yankin Leeuwarden, Friesland da ke ƙasar Netherlands.

Oyiza, ta ce ta yi kutse ne a shafin Hisbah a matsayin martani ga abin da ta ƙira “cin mutuncin mata” da hukumar ke yi.

Ta wallafa a shafinta cewa, “Barkanku da safiya jama’a, na kawo muku labari mai daɗi. Hukumar Hisbah ta Kano, waɗanda ake ganinsu da ƙima da kuma masu bayar da tarbiyya, sun shiga wani shafin batsa da wasu masu kutse suka wallafa kwanakin baya. To, yanzu mun tona asirin munafukai.”

Kazalika, matashiyar ta buƙaci Hisbah ta nemi gafarar matan da ta ci zarafinsu tare da ba su diyyar Naira 500,000 kowannensu kafin ta saki shafin nasu.

Sai dai bamu tabbatar da ikirarin matashiyar ba.

Ko da aka tuntuɓi shugaban sashen fasaha na Hisbah, Sani Zailani, ya ce ba shi da masaniya kan buƙatar matashiyar.

“Ba mu ga sakon wannan mata ba, amma za mu duba lamarin kuma za mu ɗauki matakin da ya dace,” in ji shi.

Leave a Reply