Ƙassr Ghana ta ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya da Amurka

0
71
Ƙassr Ghana ta ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya da Amurka

Ƙassr Ghana ta ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya da Amurka

Ghana ta sa hannu kan wata yarjejeniyar samar da nukiliya ta hanyar amfani da fasahar makamashin NuScale da wani kamfanin Amurka, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana a ranar Alhamis, a daidai lokacin da ƙasar ke yunƙurin kafa tashar makamashin nukiliya ta farko.

Kamfanin Makamashin Nukiliya na Ghana da Regnum Technology Group na Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tura wata ƙaramar na’urar sarrafa makamashin NuScale VOYGR-12 (SMR) zuwa babban taron Amurka da Afirka kan makamashin nukiliya a Nairobi.

Na’urorin SMRs dai sun fi ƙanƙanta idan aka kwatanta da irin waɗanda ake amfani da su a yanzu, kuma ana iya ƙera su a masana’anta. Amma akwai tambayoyi masu yawa game da ko za a ringa kasuwancinsu.

Amurka na ƙoƙarin inganta fasahohin da take ɗauka a matsayin makamashi mara gurɓata muhalli, kana ta sayar da su ga ƙasashe masu tasowa.

Gwamnatin Shugaba Joe Biden ta yi imanin cewa makamashin nukiliyar da ke samar da wutar lantarki kusan babu hayaƙi a ciki, sannan yana da matukar tasiri wajen yaƙi da sauyin yanayi.
Makamashin nukiliya, a ɗaya ɓangaren kuma yana samar da sharar nukiliya ta dindindin.

Kamfanin NuScale shi kaɗai yake da lasisin ƙera na’urar SMR a Amurka. A bara ne ya soke aikinsa ɗaya tilo a Amurka saboda hauhawar farashi.

Sauran takwarorin kamfanin da suka nemi aikin sun haɗa da kamfanin EDF na ƙasar Faransa da kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ta China, kamar yadda wani jami’in ma’aikatar makamashi a Ghana ya bayyana a watan Mayu.
Burin kawar da iskar Carbon

KU KUMA KARANTA:Matasan Ghana miliyan 1.9 ba su samu ilimi ko aiki ko wani horo ba – Rahoto

Kamfanin Kepco na Koriya ta Kudu da reshansa na makamashin nukiliyar da kuma ROSATOM na Rasha su ma suna daga cikin waɗanda suka fafata a neman kwantiragin da ake sa ran za ta kwashe tsawon shekara goma masu zuwa, in ji jami’in.

“Ghana da ƙasashen Afirka da dama na neman makamashin nukiliya don cim ma muraɗun tattalin arzikinsu tare da tsaron makamashi, da kuma kawar da iska mai gurɓata muhalli,” in ji Aleshia Duncan, mataimakiyar sakatariyar ma’aikatar makamashi ta Amurka da ke kula da haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

“Yana da matuƙar muhimmanci Amurka ta ci gaba riƙe matsayinta na abokiyar hulɗa mai ƙarfi ta hanyar ba da ingantattaun fasahohi da albarkatunta don tabbatar da nasarar samar da makamashin nukiliya a faɗin nahiyar.”

Leave a Reply