Mahaifin Daraktan Neptune Prime, Aisha Auyo, ya rasu

0
163
Mahaifin Daraktan Neptune Prime, Aisha Auyo, ya rasu

Mahaifin Daraktan Neptune Prime, Aisha Auyo, ya rasu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mahaifin Aisha Musa Auyo, Darakta, Neptune Prime Network, ya rasu. Farfesa Musa Abdu Auyo, ya rasu yana da shekaru 63. Farfesa Auyo ya rasu da sanyin safiyar ranar Talata, 27 ga watan Agusta a gidansa dake rukunin gidajen ma’aikata na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK quarters).

Za a yi jana’izarsa a yau Talata bayan Sallar Azahar da misalin ƙarfe 1:00 na rana a Masallacin Juma’a na BUK.

Kafin rasuwarsa, Farfesa Auyo yana aiki da sashen Laburare da Kimiyyar Watsa Labarai na Jami’ar Bayero Kano (BUK). Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya tara da kuma jikoki tara. Daga cikin ‘ya’yansa akwai Misis Aisha Musa Auyo, Darakta na Neptune Prime.

KU KUMA KARANTA: Mahaifiyar Mawallafin Neptune Prime, Hassan Gimba, ta rasu tana da shekara 85

Shugaba kuma mawallafin jaridar Neptune Prime (Publisher/CEO) Dakta Hassan Gimba, da ɗaukacin ma’aikatan Neptune Prime Network suna miƙa saƙon ta’aziyya ga Aisha Musa Auyo da sauran iyalan mamacin da kuma al’ummar BUK bisa ga wannan babban rashi.

Allah ya jiƙansa da rahama ya sa Jannatul Firdausi ce makoma.

Leave a Reply