Wasu ɓata-gari a Kaduna sun fasa banki da lalata motoci

0
100
Wasu ɓata-gari a Kaduna sun fasa banki da lalata motoci

Wasu ɓata-gari a Kaduna sun fasa banki da lalata motoci

Daga Ali Sanni

Wasu ɓata-gari ɗauke da tutar ƙasar Rasha sun shiga cikin masu zanga-zangar yunwa, tare da fasa wani banki a Jihar Kaduna.

Zanga-zangar dai ta rikiɗe zuwa tashin hankali a rana ta biyar a jihar, inda wasu ɓata gari suka kai hari banki a yankin Tudun Wada na Kaduna.

Ɓata garin sun lalata motocin ma’aikatan bankin sannan suka sace kayayyakin kuɗi masu tarin yawa.

Gwamnan jihar, Uba Sani, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin Kaduna da Zariya, biyo bayan tashe-tashen hankula da aka samu.

Tun daga wannan lokacin, jami’an tsaro suka shiga tarwatsa ɓata garin dake ƙoƙarin satar kayan mutane da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

A ranar Alhamis ne, aka kama aƙalla mutum 25 da suka fasa shagunan mutane tare da sace musu kayayyaki a ranar farko na zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa a jihar.

Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali a yankin Kaduna ta Arewa da wasu sassan Kaduna ta Tsakiya, yayin da yankin Kaduna ta Kudu ke cikin kwanciyar hankali.

Tuni tituna a Jihar Kaduna, sun zama fayau babu mutane tun bayan saka dokar hana fita.

Mazauna Kaduna sun yaba wa gwamnan jihar bisa saka dokar.

Leave a Reply