Zanga-Zanga: BUK ta dakatar da koyarwa zuwa wani lokaci
Daga Ali Sanni
Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da dakatar da ɗaukar darusa zuwa wani lokaci, sakamakon zanga-zangar adawa da yunwa da ake ci gaba da yi a faɗin ƙasa.
Wata sanarwa da Jami’ar ta fitar ranar Litinin, ta ce ta ɗauki matakin ne bayan zama datayi da duba batun zanga-zangar da ake yi a jahar.
“Mun damu da lafiyar ɗaliban mu da tsaron su da kuma dukiyoyinsu, shi ya sa muka ɗauki wannan matakin.
KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: An sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya
“Muna kira ga ɗaliban da ma’aikatanmu da su ci gaba da kula da irin zirga-zirgar da za su yi a wajen Jami’a domin kaucewa shiga hatsari.”
Jami’ar ta kuma shawarci ɗaliban da ke zaune a cikin makarantar da su kwantar da hankalinsu, sannan su kasance masu bin doka da oda.
Kazalika, Jami’ar ta bayar da tabbacin komawa ɗaukar darusa da zarar al’amura sun daidaita a jihar.