Za a fuskanci yunwa mai tsanani a arewa maso gabashin Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

0
34
Za a fuskanci yunwa mai tsanani a arewa maso gabashin Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya
https://collect-trump-cards.us/cgacor/
https://cttechnologynews.us/sgacor/
https://collect-trump-cards.us/vendor/
https://cutetimes.com/wp-admin/
https://carpetvacuumcleaner.com/jjs/
https://collect-trump-cards.us/generator/
https://cttechnologynews.us/product/
https://collect-trump-cards.us/thai/
https://cutetimes.com/dogol/
https://carpetvacuumcleaner.com/assets/
https://communio-vocation.com/
https://communio-vocation.com/jasa/
https://communio-vocation.com/vendor/
https://communio-vocation.com/admin/
https://antollino.com/js/
https://allthaicasino.com/filman/
https://allthaicasino.com/sgacor/
https://dreamsinsider.org/admin/
https://dreamlandgurkha.co.uk/wp-content/
http://dreammerch.net/wp-content/terbaru/
http://dreammerch.net/js/
https://adelrugs.com/film/
https://adelrugs.com/admin/
https://188.date/assets/
https://amjcorporation.co.uk/balajar/
https://amjcorporation.co.uk/sgacor/
https://blocktechy.com/sgacor/
https://blogsane.com/css/
https://bloomingpotcbd.com/xixi/
https://allthaicasino.com/
https://dreamsinsider.org/
https://dreamlandgurkha.co.uk/
http://dreammerch.net/
https://adelrugs.com/
https://188.date/
https://amjcorporation.co.uk/
https://blocktechy.com/sgacor/
https://blogsane.com/site/
https://bloomingpotcbd.com/vendor/
https://bloomingpotcbd.com/
https://blogsane.com/
https://blocktechy.com/

Za a fuskanci yunwa mai tsanani a arewa maso gabashin Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana fafutukar tara isassun kuɗaɗe don magance matsalar ƙarancin abinci a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Jami’ai sun ce ƙaruwar tashe tashen hankula a duniya sun sa ƙasashen da ke neman taimakon gwagwarmayar nema wa kansu mafita.

Koke-koken yara masu fama da larurar tamowa sun cika wani asibiti da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda suke jira a yi musu jinyar ceton rai. Asibitin da ke garin Dikwa na da tazarar kilomita 90 daga tsakiyar babban birnin jihar.

An yi jinyar yara fiye da 300 a asibitin a wannan shekarar, kuma sabbin marasa lafiya na zuwa a duk rana. Mai’akatan jin ƙai sun ce ba su da isasshen wurin kula da dukkan marasa lafiyar.

Aliyu Muhammad Sani, shi ne jami’in kula da fannin masu larurar tamowa a asibitin, ya ce akwai majinyata sama da 45 da ke jira a kwantar da su asibitin, “abin da mu ke yi shi ne idan muka je zagayen duba marasa lafiya muka ga cewa akwai waɗanda suka murmure, da waɗanda suka warke, to sai mu sallamesu, a cewarsa.

KU KUMA KARANTA:Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kaɗa ƙuri’a kan tsagaita wuta a Gaza

Amma ga duk yaro ɗaya da aka sallama, jami’ai sun ce akwai kusan wasu 10 da ke jiran gurbinsa a asibitin. Kuma tsananin yanayin ciwo ne zai sa a tantace wanda ya cancanci a kwantar da shi.

Zainab Musa, wacce rikici ya raba da matsugunninta shekaru 10 da suka wuce, tana zama a Dikwa. Ta ce ana jinyar ɗaya daga cikin tagwayen ‘ya’yanta.

“Dana ya kamu da rashin lafiya saboda yunwa, ba na iya cin abinci yadda ya kamata don in shayar da su duka biyun. Amma a nan yanayinmu ya inganta, suna ciyar da ni sau uku a rana.”

Yayin da ake da ƙiyasin yara miliyan biyu da ke fama da larurar tamowa mai tsanani, asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya na UNICEF ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu a duniya da ta fi yawan yara da suka tsumbure.

Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a kowace sa’a, yara 100 ‘yan ƙasa da shekaru biyar a Najeriya ke mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki kuma kashi 20 cikin 100 na yara da ke fama da larurar ne kaɗai ke samun jinya.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki ba, za a ga mummunan sakamako na ƙarancin abinci a wurare irin wannan.

Jami’ai sun ce matsalar ƙarancin abinci da matsalar rashin abinci mai gina jiki, su ne illolin tashe tashen hankulan ‘yan bindiga da aka daɗe ana yi a yankin, da sauyin yanayi da kuma manufofin gwamnati da suka sanya farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi.

Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ya haura kashi 40 cikin 100, a cewar ofishin ƙididdiga na ƙasar.

A watan Mayu, Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin Najeriya suka ƙaddamar da shirin neman gudummuwar dala miliyan 306 don magance matsalar ƙarancin abinci ga mutane kimanin miliyan 5 a jihohin da rikicin ya fi shafa.

Amma jami’ai sun ce gudummawar da ake bayarwa na raguwa.

“Idan aka yi la’akari da yanayin tallafin da Najeriya ke samu a cikin shekaru 10 da suka gabata, za a ga raguwar kuɗaɗen da ake samu sosai, saboda batun ba da fifiko ya shigo. Yawan rikice-rikice na ƙaruwa kusan a duk rana, ko wata-wata, ko shekara-shekara,” kamar yadda Mohamed Malik kodinetan Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin ya bayyana.

Amma a Dikwa, ƙungiyoyin agaji na taimaka wa dubban mutane su yi noman abinci a gida ta amfani da hanyoyin da suka dace da yanayin.

“Waɗanda ke bin tsarin sun sami amfanin gona da yawa daga filayen da suka noma, sun nema wa kansu hanyoyin samun sauƙin rayuwa, ta yadda za su tabbatar da samun abinci,” a cewar Khalifa Muhammad, na ƙungiyar ‘Mercy Corps Agricultural and Livestock’.

A ranar Litinin 8 ga watan Yuli, Najeriya ta sanar da shirin cire haraji kan wasu kayayyakin abinci da suka haɗa da alkama da masara domin samun farashi mai sauƙi.

Amma in dai ba a ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki ba, jami’ai sun ce makomar miliyoyin mutane, musamman yara na tattare da rashin tabbas.