Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi ƙarin haske game da janye jami’an ‘yansandan da ke samarwa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tsaro inda ta ce an ɗauki matakin ne saboda za a yi aikin tantance yawan ‘yansandan da ke ƙarƙashin hukumar da kuma fahimtar yanayin ayyukansu tun 2015 da aka tura su yin aiki a hukumar.
Bayanin na ƙunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar inda ta ce za a tantance su ne bayan rahotannin da aka samu ta hannun sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na rundunar da ke nuna cewa ana amfani da ‘yansandan da ke aikin samar da tsaro a hukumar wajen cimma wasu ƙudurori da ba aikinsu ba.
Sanarwar ta ce akwai buƙatar mutane su fahimci cewa ana tantance ma’aikatan domin martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke watsawa.
KU KUMA KARANTA:’Yan fashi sun kai hari bankuna da ofishin ’yan sanda a Kogi
Matakin, a cewar sanarwar, ya zama wajibi domin gyara matsalolin da aka gano game da yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta ganin cewa ana amfani da ‘yansandan da aka tura su samar da tsaro wajen yin kame da gudanar da bincike kan ƙararraki, wanda ƙarara ya nuna cewa sun sauka daga tsarin gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu – wani abu da ya zama dole a yi gyara a kai.
Rundunar ta ce a baya ma an gudanar da irin wannan aikin tantance ‘yansandan daga lokacin da aka kafa hukumar a 2015 kuma ‘yansandan suka koma bakin aiki bayan kammala aikin.
Sanarwar ta ce babban sufeton ‘yansanda ya umarci ‘yansandan da aka gama tantancewa su gagauta komawa bakin aiki.
Kazalika rundunar ta ce idan har hukumar na son ƙarin jami’an ‘ya sanda da za su yi mata wasu ayyukan da ba sa cikin waɗanda babban sufeton ya amince, hukumar na iya neman izini daga shugaban ‘yansandan.









