Masana sun yi ƙira da a yi sabbin sauye-sauye ECOWAS

0
170

Masana da ƙwararru sun yi nazarin cewa ƙungiyar Haɓaka Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO, na buƙatar sake tsari da sauye-sauyen da za su yi daidai da manufofin ƙasashe mambobinta.
Wannan nazarin na zuwa ne bayan gaza kataɓus wajen daukar mataki akan sojojin da suka yi juyin mulki a wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar ta ECOWAS da aka daɗe ana ɗaukar ta a matsayin wadda ta fi ci gaba a Afirka.

Sai dai wasu na ganin abin yanzu ba haka ya ke ba sakamakon juye-juyen mulki da sojoji suka yi a ƙasashe daban-daban na yankin wanda ya nuna cewa ƙungiyar ba ta da hurumi ko ƙarfi wajen magance matsalolin yankin.

Masana irin su Abdourahamane Dikko sun bayyana cewa ya zama wajibi idan ƙungiyar tana son samun galaba ta nuna kishin Afirka da kuma samar da wasu sauye-sauye da za su yi daidai da manufofin ƙasashen yankin. Ya ce ta haka ne kawai ƙungiyar za ta iya samun amannar ƙasashen yankin.

KU KUMA KARANTA:Janye takunkumin ECOWAS: An dawo da wutar lantarki a Nijar

Masanan na ganin sabon shugaban ƙasar Senegal na da kusancin ra’ayi da ƙasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso, kuma fahimtar sa da gwamnatocin ƙasashen uku ka iya sa shi neman sauye-sauye a ƙungiyar ta ECOWAS a cewar Usman Dumbia wani manazarcin siyasar ƙasa da ƙasa a Mali.

Ya ce ya zama wajibi a samar da wasu sabbin sauye-sauye a cikin ƙungiyar ta ECOWAS domin sake dawo da ƙasashen nan uku cikin ƙungiyar tare da sake tunani na yin gaba-da-gaba da ƙasashen Yamma ta yadda ƙungiyar za ta sami martaba da daraja a idanun duniya, na iya faɗa aji kuma haka na iya yiwuwa.

Jinkiri da sakaci na ƙin hoɓɓasa daga ɓangaren ƙungiyar ECOWAS din wajen ciyar da yankin yammacin Afirka gaba na daga cikin dalillan zubewar martabar ta don haka masanan ke ganin akwai buƙatar a sake lale a yi nazari akan abubuwa da yawa.

Ana ganin tsakanin ƙasashen ƙungiyar yammacin Afirka wasu na tufka wasu kuma na warware ra’ayin tafiyar da ita, masanan na ganin da ba don haka ba da tuni ƙungiyar ta samar da mafita akan makomar ƙasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso.

Leave a Reply