NDLEA ta kama wiwi da ake shirin kaiwa ƙasar Qatar

0
176

Jami’an Hukumar da ke Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Najeriya NDLEA sun kama wata mata kan zarginta da yunƙurin fitar da ɗauri 20 na tabar wiwi.

A sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce matar mai suna Chidinma Chinenye Agbazue mai shekara 35 ta ɓoye kilo 10,70 na tabar wiwin a cikin salak ɗin Abacha da busassun ganyayyaki.

Matar wadda aka kama a filin jirgin Murtala Muhammmed da ke Legas, ta yi niyyar kai tabar wiwin birnin Doha na Qatar, in ji sanarwar.

NDLEA ɗin ta ce binciken wucin-gadi ya nuna cewa Chidinma na zaune ne a Qatar amma ta koma Najeriya Disamabar bara domin bikin Kirisimeti.

Hukumar wadda ta ce ta kama matar tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar DSS, ta tabbatar da cewa Chidinma ta yada zango a otel ɗin Club Dice da ke Legas inda a nan aka miƙa mata wiwin.

Baya ga Chidinma, NDLEA ɗin ta ce ta kama Nwachukwu Chinedu mai shekara 28 a Jihar Abia kan zarginsa da safarar wiwi da tramadol.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama dillali da ke sayarwa ‘yan bindiga ƙwayoyi a Zamfara da Kebbi

“A Abia, an kama Nwachukwu Chinedu mai shekara 28 a ranar Juma’a 29 ga watan Maris a Akara Ahuba, Ƙaramar Hukumar Isikwuato. Abubuwan da aka gano daga hannunsa sun haɗa da kilo 46.65 na wiwi da adadi daban-daban na tramadol da methamphetamine da rohypnol da tsabar kuɗi N71,500,” in ji sanarwar.

Haka kuma NDLEA ɗin ta ce ta kama wata mota ƙirar Volkswagen kan hanyar Ondo ɗauke da kilo 127.5 na wiwi.

Hukumar ta ce akwai wata mai shekara 30 mai suna Chinasa Christopher wadda aka kama da kwalabe 400 na maganin tari mai ɗauke da kodin a Sabon Garin Kano.

Leave a Reply