Wakiliyar MƊD ta buƙaci a ƙaƙaba wa Isra’ila takunkuman samun makamai kan kisan kare dangin da take yi a Gaza

0
141

Wata ƙwararriya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shaida wa hukumar kare hakkin bil adama ta duniya cewa ta yi imanin cewa yakin da Isra’ila ta yi a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai na kisan ƙare dangi, ta kuma yi kira ga ƙasashen da su gaggauta ƙaƙaba takunkumi ciki har da na hana ta samun makamai.

“Na gano cewa akwai dalilai masu ma’ana da za a yarda da cewa ana yi wa Falasɗinawa kisan ƙare dangi a Gaza,” a cewar Francesca Albanese, mai kare hakkin bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta musamman a yankunan da aka mamaye, kamar yadda ta shaida wa hukumar kare hakkin bil adama ta MƊD a Geneva.

Leave a Reply