Yaran Najeriya sun cancanci samun ilimi cikin kwanciyar hankali – UNICEF

0
71

Asusu tallafa wa ƙananan yara na majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya yi Allawadai da harin baya-bayan nan da aka kai kan wata makaranta a jihar kaduna.
A sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, wakilin UNICEF a Najeriya, Christian Munduate, ya bayyana takaici game da harin, inda yace yaran Najeriya sun cancanci samun ilimi a yanayi na lumana.

Wakilin asusun na UNICEF ya ƙara da cewar, kamata ya yi makarantu su kasance killatattun wurare na neman ilmi da ci gaba amma ba bigirorin tsoro da tashin hankali ba.

An ruwaito sanarwar na cewa, “na yi matuƙar baƙin ciki da damuwa game da wannan rahoto na sake sace ɗalibai a jihar Kaduna. Yawaitar irin waɗannan al’amura a faɗin Najeriya alama ce ta tashin hankalin da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa masu tsauri daga dukkanin matakan gwamnati da al’umma. Kamata ya yi makarantu su zama keɓaɓɓun wuraren neman sani da ci gaban ɗan adam, amma ba bigirorin tsoro da tashin hankali ba”.

KU KUMA KARANTA:Ɗalibi ɗaya ya kuɓuta daga cikin ‘yan makarantar da ‘yan bindiga suka sace a Kaduna

“Satar ɗalibai na baya-bayan nan, kamar waɗanda suka gabace shi, abin allawadai ne kuma wani ɓangare ne na salon kai hare-hare akan cibiyoyin ilimi, musamman ma a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, inda ƙungiyoyin ‘yan bindiga suka zafafa kai hare-hare da yin garkuwa da mutane. Kwana guda kafin aukuwar wannan lamari, jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya ya zanta akan satar ɗimbim mata da ‘yan mata harma samari da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka yi a jihar Borno”.

“Asusun tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, da haɗin gwiwar wasu jami’an Najeriya na taimakawa wajen kwantar da hankulan iyaye da dangin yaran da aka sace.

UNICEF ya duƙufa wajen yin haɗin gwiwa da gwamnatoci da al’umma da ƙungiyoyin ba da agaji domin magance dalilan da ke jefa yara cikin tashin hankali tare da ba da kariya ga makarantu daga kowace irin barazana da tashin hankali.

Leave a Reply