An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

0
97

Akeredolu ya rasu a ƙasar Jamus a ranar 27 ga watan Disambar bara bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 67.

An gudanar da jana’izar tsohon Gwamnan jihar Ondo marigayi Rotimi Akeredolu a mahaifarsa ta Owo da ke jihar wacce kudu maso yammacin Najeriya.

A ranar 27 ga watan Disambar bara Akeredolu ya rasu a Jamus inda ya je neman magani saboda fama da rashin lafiya.

KU KUMA KARANTA:Tashin farashin dala na daga cikin manyan matsalolin Najeriya – ƙwararru

An fara jana’izar ce da taron addu’o’i a Mujami’ar St. Andrews kafin daga bisani a binne shi.

Manyan jami’an gwamnatin jihohi da na tarayya da suka halarci taron janai’zar sun haɗa mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettimah.

Kazalika Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Oyo Seyi Makinde da shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje duk sun halarci taron jana’izar.

Yayin jawabinsa, Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ya gaji Akeredolu, ya kwatanta marigayin a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwarsa don kare jama’a.

Leave a Reply