Jamhuriyar Nijar ta gaza biyan bashin fiye da dala miliyan ɗari biyar tun da sojoji suka kifar da gwamnatin farar-hula a watan Yulin da ya gabata, a cewar ƙungiyar da ke sa ido kan kuɗaɗen yankin Yammacin Afirka.
Umoa-titres, wadda ke lura da Harkokin Kuɗi na Ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka (WAEMU), ta wallafa sanarwa guda takwas tun farkon wannan shekara da ke jan hankalin masu zuba jari cewa Nijar ta “gaza cika alƙawuran da ta ɗauka na kasuwar hada-hadar kuɗi ta Gwamnati”.
Ta ce ana bin ƙasar bashin da ya kai CFA biliyan 313 ($515m) tun da sojoji suka ƙwace mulki a watan Yuli wanda ya kamata ta biya ranar 16 ga watan Fabrairu.
“Ya kamata a sani cewa wannan batu na gaza biyan bashi ya faru ne a lokacin da shugabannin ƙasashe da gwamnatoci na ƙungiyar da ke lura da Harkokin Kuɗi na Ƙasashen Yammacin Afirka suka sanya wa Nijar takunkumai kan harkokin kuɗi,” kama yadda Umoa-titres ta bayyana ranar Litinin.
Umoa-titres ce ke da alhakin gudanarwa da tallata harkokin kuɗi na Yammacin Afirka, waɗanda suka haɗa ƙasashe takwas da ke amfani da CFA franc a matsayin kuɗinsu — Ivory Coast, Senegal, Togo, Burkina Faso, Mali, Guinea-Bissau, Nijar da Benin.
KU KUMA KARANTA: Za mu ci gaba da tattaunawa da Nijar domin samun maslaha – ECOWAS
A makon jiya, cibiyar Moody’s da ke auna ƙarfin iya biyan bashin ƙasashe da tattalin arzikinsu ta rage matsayin Nijar na iya biyan bashi daga matakin Caa2 zuwa Caa3 karo na uku a jere tun da sojoji suka yi juyin mulki.
“Takunkuman da aka sanya wa ƙasar tun ƙarshen watan Yulin 2023 sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi sun ta’azzara mawuyacin hali na tattalin arziki sannan sun yi tarnaƙi ga gwamnati wajen iya biyan bashi,” a cewar cibiyar.