Mutum 6 sun rasu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Ebonyi

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a jihar Ebonyi, ta tabbatar da rasuwar mutum shida a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Afikpo zuwa Abakaliki a jihar.

Kwamandan hukumar a jihar, Igwe Nnabuife, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abakaliki cewa hatsarin ya rutsa da mutum 17.

Nnabuife, ya ce mutum shida sun mutu, yayin da 11 suka samu munanan raunuka.

A cewarsa, hatsarin ya rutsa da motoci uku da kuma wasu manyan motoci biyu.
“Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11:50 na safe a yankin Onuwedu, da ke Karamar Hukumar Ezza ta Kudu a Ebonyi.

“Hatsarin ya faru ne, sakamakon gudun wuce kima. “An kai gawar waɗanda suka mutu Asibitin Koyarwa na Tarayya na Alex Ekwueme da ke Abakaliki.

KU KUMA KARANTA: Mummunan hatsarin Mota ya ci rayukan mutane 18 a hanyar Kano zuwa Kaduna

“Waɗanda suka jikkata likitoci na ba su kulawa.

“Muna bai wa direbobi shawara su kasance masu haƙuri yayin tuƙi. Su kasance masu bin dokokin hanya, hakan na da matukar muhimmanci. A guji tukin ganganci don ceto rayuka,” in ji Nnabuife.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *