Ƙungiyoyin dattawan arewa da na Ibo, sun koka kan yawan yawace-yawacen Tinubu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya da takwararta ta Ohanaeze Ndigbo mai kare muradun al’ummar Igbo da wasu ƙungiyoyin farar hula sun bayyana rashin jin daɗinsu game da tafiya zuwa Paris da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi daidai lokacin da ƙasar ke fama da ƙaruwar matsalar tsaro.

A ranar Laraba 24 ga watan Janairu ne shugaba Tinubu ya tafi zuwa Faransa domin wata ziyara ta ƙashin kai.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar gabanin tafiyar, ta ce Tinubu zai koma Najeriya cikin makon farko na watan Fabarairu.

Sai dai ƙungiyoyin a hirarsu da jaridar Daily Trust sun koka cewa babu gaskiya cikin sanarwar tafiyar la’akari da yadda aka ƙira tafiyar ta “ƙashin kai”.

Matakin ƙungiyoyin na zuwa ne bayan da shi ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya soki Tinubu inda ya bayyana shakku game da maƙasudin tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake fuskantar ƙaruwar matsalar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta’azzara.

KU KUMA KARANTA: Ganganci ne Atiku ya ce Tinubu ba ya aikinsa yadda ya kamata – Fadar shugaban Najeriya

Sai dai Fadar shugaban ƙasar ta ce duk da cewa Tinubu ba ya ƙasar, yana aiki tuƙuru domin kawo sauƙin matsalolin kuma yana bai wa hukumomin tsaro dukkanin goyon bayan da suke buƙata domin samun nasara kan masu aikata miyagun laifuka da nufin fitar da Najeriya daga halin rashin tsaron da take ciki.

Tinubu dai ya sa ƙafa ya fice daga ƙasar yayin da ake tsokaci game da jerin hare-haren da aka kai a Filato da sace-sacen jama’a a Abuja, babban birnin ƙasar da kuma hari na baya-bayan nan na sace ɗalibai da malaman makaranta a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriyar ta ce tafiyar ta Tinubu zuwa Paris a irin wannan yanayi da ake ciki a kasar manuniya ce cewa shugaban ya duƙufa ne wajen cimma ƙudurorinsa na kashin kai a maimakon bai wa yan Najeriya kwarin gwiwa a lokacin da suke bukatar hakan.

Daraktan yada labarai na ƙungiyar, Abdulazeez Sulaiman ya ce ƙungiyar tana ganin matakin na shugaban ƙasar na tabbatar da damuwar da ake nunawa cewa Najeriya ta faɗa cikin matsalar rashin shugabanci na gari da rashin nuna damuwa da tausayi.

A nata ɓangaren, ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi allah-wadai da tafiyar ta shugaba Tinubu zuwa Paris a halin taɓarɓarewar tsaro da sauran ƙalubale da ake ciki.

Babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce bulaguron da Tinubu ya yi na zuwa ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi.

Isiguzoro ya yi ƙira ga Tinubu da ya yi wa ‘yan Najeriya bayani dalilin yin irin waɗannan tafiye-tafiye.

Shi ma shugaban ƙungiyar tabbatar da jagoranci na gari, GGT, Mista Tunde Salman ya ce da alama shugaba Tinubu ya bai wa wasu manyan jami’ai har da mataimakin shugaban ƙasa damar tafiyar da al’amuran.

Ya ba da misali da wani ƙwarya-ƙwaryan taro da aka shirya kan tsaro game da ƙaruwar matsalar a arewacin Najeriya, inda mataimakin shugaban ƙasa da ministocin tsaro suka zama masu taka rawa sosai a taron.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *