Da ɗumi-ɗumi: Mun kama wanda ya kashe Nabeeha – ‘Yansanda

0
222

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tabbatar da kama wanda ya sace Nabeeha Al-Kadriyah da wasu mutane da ake zargi da hannu cikin satar mutane.

Kakakin ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Cikin sanarwar ya ce a wani samame da suka akai wani otel a yankin Tafa, a ranar 20 ga watan Janairu, sun cafke wani da ake ƙira Bello Mohammed, ɗan shekara 28, mutumin Zamfara.

“An kama shi da kuɗi da suka kai naira miliyan 2 da dubu dari biyu da hamsin, wanda muke zargin kuɗin fansa ne da wani wanda aka kama ɗan uwansa ya biya a tsukukun yankin.

KU KUMA KARANTA: ‘Ba ‘yansanda ba ne suka kuɓutar da ‘ya’yanmu, biyan kuɗin fansa muka yi’ – Iyayen Nabeeha

“Yayin gudanar da tambayoyi, mun gano cewa yana cikin gungun mutane da suka kama iyalan wani lauya da ake ƙira Ariyo a yankin Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairu. Waɗanda suka kashe wata matashiya da ake ƙira Nabeeha,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Wanda ake zargin in ji sanarwar ya yi tayin miliyan guda ga shugaban ‘yan sandan yankin, sai dai DPO bai karɓi kuɗin ba, ya yi aikinsa yadda ya kamata.

Leave a Reply