Daga Ibraheem El-Tafseer
Wani jirgin sama da ke kan hanyarsa ta zuwa Amurka, ANA, dole ya sauya akala ya koma Tokyo, bayan wani fasinja da ya bugu mai shekara 55 ya gartsa wa wata ma’aikaciyar jirgin cizo a hannu har ya yi mata ɗan rauni.
Mai magana da yawun kamfanin jirgin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP aukuwar lamarin.
A cewar kafar watsa labarai ta Japan, mutumin ya faɗa wa ‘yan sanda ya sha maganin bacci don haka ba zai iya tuna abin da ya faru ba.
Lamarin shi ne na baya-bayan nan cikin jerin matsalolin da fannin sufurin jiragen sama na ƙasar ya fuskanta a ‘yan kwanakin nan.
Jirgin da ke ɗauke da fasinjoji 159 na saman tekun Pacific a lokacin da lamarin ya faru, abun da ya tilasta wa matuƙan jirgin juyawa suka koma filin jirgin Haneda da ke Tokyo.
KU KUMA KARANTA: Jirgin fasinja mai taragu 21 ya yi hatsari a Indiya
Kamfanin jirgin ya ce a filin jirgin suka miƙa mutumin hannun ‘yan sanda.
A ranar asabar jirgin saman ANA da ke zirga-zirga a cikin gida a ƙasar ta Japan ya juya inda ya fito bayan an gano ɗaya daga cikin tagogin jirgin ya tsage.
Mafi munin lamarin da ya faru da jiragen sama na Japan shi ne na ranar 2 ga watan Junairu, a filin jiragen sama na Haneda lokacin da jirgin ƙasar ya yi karo da ƙaramin jirgi na masu tsaron gaɓar teku.
Duka fasinjoji 379 da ke cikin jirgin sun kuɓuta, bayan ya kama da wuta, amma mutane biyar cikin shida da ke ƙaramin jirgin sun mutu.