Mai ɗakin shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana kaɗuwarta kan mutuwar Nabeeha Al-Kadriyar, da ‘yan bindiga suka halaka.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Sanata Oluremi ta bayyana mutuwar Nabeeha a matsayin rashi mai matuƙar sosa zuciya inda kuma ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayiyar.
Sanata Oluremi ta kuma buƙaci ‘yan Najeriya su haɗa kansu wajen yin addu’o’i da za su kai ga sakin ‘yan’uwan Nabeeha, waɗanda har yanzu ke a hannun masu garkuwa.
Da take magana kan ƙaruwar matsalar tsaro da sace-sacen jama’a, Oluremi ta yi ƙira ga hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen hana satar jama’a su kuma yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ‘yan’uwan Nabeeha.
KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun lakaɗa wa basarake duka har ya suma saboda rashin cika kuɗin fansa
A ranar 2 ga watan Janairu Nabeeha da ‘yan’uwanta suka faɗa hannun ‘yan bindiga a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Mahaifinsu Mansoor Al-Kadriyar, wanda shi ma ya shiga hannun masu garkuwar daga bisani sun sake shi domin ya dawo gida a haɗa kuɗin fansar ‘ya’yansa.
Sai dai masu garkuwa sun ƙara kuɗin fansar tare da kashe Nabeeha bayan da aka gaza haɗa kuɗin fansar.
Sun kuma yi barazanar kashe ragowar ‘yan matan da ke hannunsu idan aka ƙi biyan su kuɗi kafin wa’adin da suka ɗiba.









