Sojojin Najeriya sun kama wani babban kwamandan IPOB a jihar Inugu

0
149

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wani babban kwamanda na ƙungiyar IPOB da wasu mutum ukun a maɓoyarsu Cocin Christ the King Catholic da ke ƙaramar hukumar Awgu a Jihar Inugu da ke kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, ta ce an samu nasarar kama mutanen ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ta yi a ranar Laraba 13 ga watan Disamban 2023.

“Dakarun rundunar GOLDEN DAWN III tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun yi nasarar kama wani kwamanda na haramtacciyar ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra ta IPOB da takwararta ta ESN, Mr Uchechukwu Akpa da wasu ƴan ƙungiyar uku,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa an samu nasarar kamen ne a yayin wani samame da aka kai lokacin da suke yin wani taro kan karɓar ragamar shugabancin ƙungiyar IPOB/ESN daga tsohon kwamandanta na jihar Inugu da yake tsare, da kuma shirin da suke yi na kai hare-hare a kan dakaru.

A yayin farmakin, Mista Uchechukwu Akpa ya samu rauni a lokacin da yake kokarin tserewa.

Sauran da aka kama su ne; Udoka Anthony Ude da Ikechukwu Ulanta da kuma Ezennaya Udeigewere.

Rundunar sojin ta kuma ce ta yi nasarar ƙwato makamai a samamen da suka haɗa da jigidar harsasai huɗu.

“Idan dai za a iya tunawa, Mista Uchechukwu Akpa shi ne mataimakin tsohon kwamandan mai suna Chocho, wani fitaccen mai aikata laifi ɗan ƙungiyar IPOB/ESN wanda tun da farko ya tsere zuwa Jihar Binuwai saboda tsananin ayyukan da yake yi, wanda aka kama shi a baya-bayan nan.

KU KUMA KARANTA: Amurka za ta taya sojojin Najeriya rage harin kuskure

“A yanzu haka su ma sauran masu laifin da aka kama suna tsare don yin bincike a kansu,” a cewar sanarwar.

Kazalika rundunar soji ta ce bayan wannan kamen, ta sake kai wani samamen a ranar Alhamis 14 ga watan Disamban nan a wata maɓoyar tasu da ke Nenwe, a ƙarmar hukumar Agwun ta Jihar Enugu, inda ta ƙwace bindigogi da harsasai da sauran muggan makamai.

Runudnar sojin ta gode wa hukumomin tsaron da suka ba da haɗin kai wajen samun nasarar wannan aiki, da yaba wa al’ummar yankin kudu maso gabashin ƙasar kan haɗin kan da suke baiwa jami’an tsaro da bayanan da suke sa ana kama masu laifi.

Leave a Reply