Za mu jajirce har sai an yi wa mutanen Tudun-Biri adalci – Sarkin Musulmi

0
100

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya buƙaci a yi adalci ga mutanen da harin sojin ƙasar ya kashe a garin Tudun-Biri da ke ƙauyen ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda sama da rayuka 100 suka salwanta.

Sarkin ya faɗi haka ne a wurin taron murnar cika shekaru 25 da darewar Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad kan karagar mulki a fadarsa da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna a wannan Juma’ar.

Ba wai kawai taron taya sarki murna ba ne ya kawo mu nan, har da yin addu’a ga masarautar da kuma rayukan mutanen da suka salwanta a Kaduna. Za mu yi matsin lamba don ganin an yi adalci ga mutanen inji Sarkin Musulmin.

Wannan na zuwa ne bayan jama’a da dama a Najeriya sun yi ta korafi kan cewa, ba su ji komai daga bakin Sarkin Musulmin ba tun bayan aukuwar harin na kuskure kan mutanen da ke halartar taron maulidi a garin na Tudun-Biri.

Tuni gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, lallai za a hukunta duk wanda ke da hannu a wannan harin, inda har mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya ziyarci mutanen da ibtila’in ya shafa a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.

Mataimakin shugaban ƙasar ya sanar da shirin gwamnatin tarayya na sake gina garin na Tudun-Biri da kuma ba su tallafi.

Leave a Reply