An kama mutanen da suka jagoranci harin Sierra Leone — Shugaba Bio

0
138

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama “akasarin shugabannin” waɗanda suka yi ƙoƙarin hargitsa ƙasar.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa ‘yan ƙasar ta gidan talbijin ranar Lahadi da maraice.

“An kama akasarin shugabanninsu. Ana ci gaba da gudanar da bincike,” kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai barikin sojoji inda suka fasa wurin da ake ajiye makamai. Haka kuma maharan sun fasa gidan yarin ƙasar inda suka saki fursunoni.

Shugaba Bio ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an hukunta waɗanda aka kama da laifi bayan an bi ƙa’ida.

KU KUMA KARANTA: An saka dokar hana fita a ƙasar Saliyo

Ya kuma yi ƙira ga ‘yan ƙasa su haɗa kansu inda ya ce “ƙarfinmu ya dogara ne kan haɗin kanmu” inda kuma ya tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa gwamnatinsa za ta samar da zaman lafiya da tsaro a cikin ƙasar.

Ƙungiyar ECOWAS ta nuna rashin jin daɗinta kan lamarin da ya faru a Saliyo a ranar Lahadi.

“Ƙungiyar ECOWAS ta ji labarin wannan abin kyamar da wasu mutane suka ɗauki makamai da niyyar kawo cikas ga zaman lafiya da kuma dokar da ƙundin tsarin mulki ya tanada a Saliyo,” kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwa.

“ECOWAS ta yi Allah wadai da wannan lamarin inda take ƙira kan a kama tare da hukunta waɗanda suke da hannu a lamari. ECOWAS na ƙara jaddada cewa ba za ta lamunci sauyin gwamnati ba bisa ƙa’idar ƙundin tsarin mulki ba.”

Leave a Reply