Ban kashe naira miliyan 400 wajen tafiya ƙasashen ƙetare ba – Lawal

0
223

Gwamnan jihar Zamfara dake Najeriya Dauda Lawal ya yi watsi da zargin da aka masa cewar ya hallaka kuɗin jiharsa da suka kai naira miliyan 400 wajen tafiye tafiye zuwa ƙasashen ƙetare.

Wata jaridar da ake wallafawa a kafar intanet ta wallafa labarin, inda tace gwamnan ya kashe sama da naira miliyan 170 zuwa ƙasashen ƙetare da wasu naira miliyan 220 wajen tafiye tafiye a cikin gida da kuma wasu kusan naira miliyan 7 a kan jami’an tsaro masu zaman kansu dake kare lafiyarsa a cikin watanni 3 da suka gabata.

Mai magana da yawun gwamnan Suleiman Bala Idris ya bayyana labarin a matsayin mara tushe ballantana makama, yayin da ya zargi wasu ‘yan siyasa da kokarin batawa gwamnan suna.

Idris ya danganta rahotan da rashin fahimtar takardun kasafin kuɗin jihar, waɗanda suka kunshi rahotan watanni 3 na farko wanna shekaran da kuma na 2 da na 3 waɗanda gwamnatin da ta gabata ta fara kashewa, kafin na wannan gwamnati mai ci.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Zamfara ya jagoranci taron majalisar zartaswar jihar, ya karɓi rahoton kwamitin ‘yan fansho

Mai magana da yawun gwamnan yace domin tabbatar da gaskiya da kuma adalci a ƙarƙashin gwamna Lawal, jihar Zamfara na wallafa ayyukan ta a shafin gwamnati dake intanet yadda kowa zai iya zuwa ya ganewa idansa da kuma sanin sahihin abinda ke faruwa a jihar.

Idris yace tun bayan hawa karagar mulkin jihar Zamfara, sau 3 kacal Dauda Lawal ya tafi aiki ƙasashen ketare, waɗanda suka haɗa da zuwa taron majalisar ɗinkin duniya a Amurka da tafiya Kigali dake ƙasar Rwanda domin halartar taron Hukumar ci gaba da ta majalisar ɗinkin duniya da kuma tafiya Abidjan dake ƙasar Cote d’Ivoire, domin ganawa da shugaban bankin raya ƙasashen Afirka ta AfDB, Akinwumi Adeshina.

Mai magana da yawun gwamnan yace tafiya taron majalisar ɗinkin duniya da kuma ganawar da gwamnonin arewa maso yamma da suka yi da shugaban AfDB a Abidjan kawai gwamnatin jihar Zamfara ta biya, yayin da taron Kigali UNDP ta ɗauki nauyi.

Leave a Reply