Ambaliya ta kashe mutane 50 a Somaliya tare da raba dubu 700 da muhallansu

0
156

Ambaliyar ruwa a Somaliya ta kashe mutane 50 tare da raba kusan dubu 700 daga gidajensu, kamar yadda wani jami’in gwamnatin ƙasar ya sanar, inda ake fargabar ruwan sama mai ƙarfi da ya fara a ranar Talata zai ƙara dagula al’amura a ƙasar.

Yankin na ƙahon Afirka na fama da ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da ambaliya da ke da nasaba da sauyin yanayi na El Nino, lamarin da ya yi sanadin asarar rayukan mutane tare da raba da dama da muhallansu, ciki har da ƙasar Somaliya, inda ruwan sama ya lalata gadoji tare da mamaye gidaje.

“Mutane 50 ne suka mutu a wannan bala’in… yayin da ta tilastawa sama da 687,235  barin gidajensu,” in ji daraktan hukumar kula da bala’o’i ta Somalia, Mohamud Moalim Abdullahi a wani taron manema labarai a ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa ” ruwan sama da ake sa ran za a yi tsakanin ranakun 21 zuwa 24 ga watan Nuwamba… na iya haifar da ambaliyar ruwa da za ta iya haddasa mutuwa da barna.”

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa ta raba mutum fiye da rabin miliyan da gidajensu a Somalia

A ranar Asabar, hukumar jin kai ta Majalisar Ɗinkin Duniya OCHA ta ce adadin mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa a Somaliya “ya kusan ninki sau biyu a cikin mako guda”, yayin da mutane miliyan 1.7 ke fama da bala’in baƙi ɗaya.

Leave a Reply