’Yan bindiga a Katsina sun kashe mutum 5, sun sace wasu 5

0
164

Wasu ’yan bindiga sun sake kai hari a ƙauyen Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina, inda suka kashe aƙalla mutum biyar.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar talata, sa’o’i 24 bayan harin da wasu mahara suka kai wa masu taron Mauludi, inda aka rawaito sun kashe aƙalla mutum 25.

Matazu da Musawa dai na makwabtaka da ƙaramar hukumar ne inda wasu daga cikin waɗanda harin masu Mauludin ya ritsa da su.

Wani mazaunin garin na Sayaya, wanda ya ce mahaifinsa na cikin waɗanda aka kashe, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun kai farmaki gida-gida, inda suka kashe biyar tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Ya ce ’yan ta’addan sun kuma yi awon gaba da dabbobi tare da kwashe wasu kayayyakin amfanin yau da kullum a yayin farmakin.

A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun harbe mutane 20 tare da jikkata wasu da dama a wajen Mauludi

Ya ce, “A ranar 6 ga watan Nuwamba, 2023, ‘yan fashin daji ɗauke da muggan makamai irin su AK-47, sun kai hari ƙauyen Sayaya, Matazu a jihar Katsina.

“Bayan samun rahoton nan take, jami’an tsaro suka wurin, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar tare da yin nasarar daƙile harin.

“Duk da haka, an harbe mutum biyar, biyu sun jikkata, sannan maharan sun yi garkuwa da mutane biyar. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Katsina a yayin da yake jajanta wa iyalan waɗanda harin ya rutsa da su, ya buƙaci jama’a da su bada bayanan da za su taimaka wajen gudanar da bincike tare da zakulo maharan.

Hare-haren ‘yan bindiga na ƙaruwa a kwanan nan a jihar Katsina duk da kirkiro jami’an sa ido da gwamnatin jihar ta yi a matsayin wani mataki na daƙile matsalar.

Leave a Reply