Afirka ta Kudu ta janye dukkan jami’an diflomasiyyarta daga Isra’ila

0
146

Afirka ta Kudu ta sanar da janye dukkan jami’an diflomasiyyarta daga Tel Aviv bayan ƙazamin harin da Isra’ila ta kai a Gaza a daren Lahadi.

Harin bama-bamai dai na ɗaya daga cikin mafi muni da Isra’ila ta yi tun bayan yakin da aka fara wata guda da ta wuce.

A cewar asibitin Al-Shifa na birnin Gaza, kimanin mutane 200 ne suka mutu.

Gwamnatin Afirka ta Kudu, wadda ta daɗe tana goyon bayan Falasɗinawa, ta yi kakkausar suka ga Isra’ila a ranar Litinin

Ministan harkokin wajen ƙasar Naledi Pandor ya shaidawa taron manema labarai cewa, Afirka ta Kudu na janye jami’an diflomasiyyarta.

KU KUMA KARANTA: Chadi ta sanar da janye jakadanta daga Isra’ila

Pandor ya bayyana cewa: “Muna matukar damuwa da yadda ake ci gaba da kashe ƙananan yara da fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba a yankunan Falasɗinawa, kuma mun yi imanin ramuwar gayyar da Isra’ila ke yi ya zama abin damuwa.

Har yanzu dai Isra’ila ba ta ce uffan ba game da wannan furuci na Afirka ta Kudu ba, amma ta dage cewa tana ƙoƙarin ganin ta rage asarar rayukan fararen hula tare da zargin Hamas da ke iko da zirin Gaza da yin amfani dda fararen hula a matsayin garkuwa.

A ranar 7 ga Oktoba, mayakan Hamas —waɗanda Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci—sun kashe mutane fiye da 1,400 a Isra’ila.

Haka kuma sun yi garkuwa da mutane sama da 230 ciki har da wani dan ƙasar Afirka ta Kudu daya wanda har yanzu ba a tabbatar da sunansa ba.

Leave a Reply