‘Saboda rashin ruwa, a dole muke shan gurɓataccen ruwa’ – Al’ummar Gaza

0
184

A ranar 9 ga watan Oktoba, mutanen Gaza sun tashi da matsananciyar wahalar ruwa wadda ta shafi mutum fiye da 650,000.

Fanfunan ruwa sun daina zuba a yankin da aka yi wa ƙawanya jim kaɗan bayan da Ministan Makamashin Isra’ila Katz ya sanar da datse musamman abubuwa kamar abinci da ruwa da kuma lantarki zuwa Gaza a matsayin wani martani ga harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Wani mazaunin Gaza Abdul Munim, mai shekara 23, ya ce lokacin da ya ji labarin, nan-take ya fara damuwa kan ‘yan biyunsa maza ‘yan wata shida.

“Yaya za mu samar da kwalabe idan ba mu da damar samun ruwa mai tsafta na sha?” kamar yadda Munim ya shaida wa TRT World.

Ɗauke wutar lantarki da Isra’ila ta yi ya sa Falasɗinawa ba sa samun ruwa da sauransu.

Isra’ila ce take riƙe da ragamar ruwan Gaza. Yayin da aka yi wa Gaza ƙawanya, Isra’ila ta daƙile hanyar ruwa da wajen sarrafa ruwan kwatami saboda ɗaukewar wutar lantarki.

Kamar yadda hukumar ruwa (OCHA) wacce ita ɗaya tilo ta rage kuma ta daina aiki a ranar 15 ga watan Oktoban saboda ƙaranci man fetur, haka zalika sauran tsofaffin tashoshin sarrafa ruwan kwatami, abin da ke jawo ƙarin ruwan kwatami shiga teku.

‘Ba mu da zaɓi’

Isra’ila ta dawo da ruwa ga yankin kudancin Gaza na wani ɗan lokaci tsawon sa’a uku a ranar Litinin. Haka zalika kamar yadda hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Gaza ta ce mutum kaso 14 cikin 100 ne suka samu ruwan da aka buɗe.

KU KUMA KARANTA: Ana tsananin buƙatar man fetur a Gaza, saboda ayyukan asibitoci — MƊD

Ƙarancin man fetur da hare-hare ta sama ya jawo tankokin ruwa sun daina aiki, kuma ruwan roba yana ƙaranci kuma ya yi tsada, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana. Galibin mutane suna samun ruwan sha ne daga ‘yan ga-ruwa da suke amfani da hasken rana wajen tsaftace ruwan kuma ana rarraba ruwan.

Cikin zaƙuwa mutane suna tona rijiyoyi a garuruwan da ke gabar teku. Dubban Falasɗinawa ne aka tilasta wa shan ruwan da ya gurɓata kuma suna haɗarin kamuwa da cututtuka da ruwa ke yaɗawa.

Yawancin mazauna Gaza suna dogaro ne da ruwan gishiri wanda ya gurbata da kwatami da ruwan teku. Ruwan kuma ya ƙunshi sinadarin Nitrates da ya samo asali daga takin zamani da kuma takin dabbobi. Aƙalla kaso 96 cikin 100 na ruwan ba ya shawuwa, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.

“Ba mu da wani zaɓi; me za ka yi? ‘Ya’yana suna buƙatar madara, suna buƙatar abinci,” in ji Munim.

“Me ya sa duniya ta yi tsit? Isra’ila ta hana mu manyan damarmakin rayuwa”.

A cewar masana na Majalisar Ɗinkin Duniya, hana mutane ruwa laifin yaƙi ne saboda ya take dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniyar Geneva. Isra’ila ta yi iƙirarin cewa ta dawo da ruwa a yankin kudancin Gaza da kuma bude Rafah don shigo da kayayyakin jin ƙai. Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, manyan motoci 20 ne ɗauke da kayan agaji ne suka shiga Gaza.

“Abin da ke faruwa a nan bai kamata a yi wa ɗan Adam ba, sannan ƙasashen duniya suna goyon bayan Isra’ila a siyance da ta fuskar ƙarfin soja da ta kowace irin hanya,” in ji Zayneb al Shalalfeh, wata jami’a a Palestinian Women Water Practitioners Network.

Al Shalalfeh ta yi bayani kan samar da ruwa inda ta ce ana samar da kaso biyar cikin 100 na buƙatar ruwa da ake da shi, kuma yana ci gaba da yin ƙasa.

“Tashar ruwan Isra’ila ta Mekorot, tana samar wa Gaza kaso 13 cikin 100 na buƙatar ruwanta ne, kimanin 53,000 a kullum. Kodayake an samu tsaiko tsakanin ranar 9 ga Oktoba zuwa 15.”

“Bugu da ƙari, akwai kamfanonin tace ruwan gishiri wanda ke samar, wanda yake karbin samar da kaso bakwai cikin 100 na ruwan Gaza, yanzu ba sa aiki. Waɗannan matatun ruwa ƙanana suna iya tace ruwan gishiri tsakanin 18,000 zuwa 32,000 a kowace rana, amma suna buƙatar lantarki da man fetur,” in ji al Shalalfeh.

Ruwan roba a kasuwa zai ƙaru. Farashin ruwan roba zai ƙaru sosai, abin da zai sa iyalai masu matsakaicin ƙarfi a Gaza ba za su iya saya ba.

Ruwa – wani makami na nuna ƙarfin iko

A tarihi, ƙarfe iko da ruwa ya kasance wani salo na masu mulkin mallaka don korar mutane daga ƙasarsu. An yi amfani da wannan salo a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, wanda Isra’ila ta mamaye tun shekarar 1967.

Kodayake an kafa yarjejeniyar Kwamitin Joint Water a shekarar 1995 tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa, Isra’ila tana da iko cewa a’a kan shirin samar da tashar ruwa ta Falasɗinawa. Babu iyaka kan adadin ruwan da Isra’ila za ta yi amfani da shi daga ƙasar da ta mamaye.

“Isra’ila ce take da iko da kaso 80 cikin 100 na albarkatun ruwa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kuma kamar yadda Yarjejeniyar Oslo ta tanada, ruwa zai ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon Isra’ila,” in ji Abdelrahman Tamimi, darakta a Palestinian Hydrology Group kuma malami a Jami’ar Arab American.

Tamimi ya yi ƙarin bayanin cewa Bayahude ɗan kama wuri zauna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan yana amfani nunki shida na ruwan sha idan aka kwatanta da ‘yan Falasɗinu, lita 350 ga kowane mutum a kowace rana, yayin da Falasɗinawa kowane mutum yana samun lita 60 ne a kowace rana, idan aka raba adadin ruwan da ake ba ta da yawan mutanenta.

“A tsawon shekara 55 na mamayar Isra’ila a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gaza, Isra’ila ce take da iko da ruwan koguna da na ƙarƙashin ƙasa kuma ta hana bunƙasa kamfanonin da matatun ruwan Falasɗinawa, kuma tana amfani da albarkatun ruwa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan ga Yahudawa ‘yan kama wuri zauna.”

A Gaza, Munim ya bayyana yanayin da ‘gudun ya da ƙanin wani’.

“Idan ƙarancin ruwa a jiki da yaɗuwar cutuka da gurɓataccen ruwa bai kashe ka ba, hare-hare ta sama zai kashe ka, saboda haka ina bakin ƙoƙari don kare iyalina da kuma tsira,” in ji shi.

“Idan gurɓataccen ruwa ya taimaka mana muka rayu yanzu, babu damuwa za a sha. Ba mu da wani zaɓi.”

Leave a Reply