Yadda wasu hatsabiban matasa uku suka sace kambu, hula da sandan sarautar sarki

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Asabar ɗin da ta gabata ta ce jami’anta sun kama Amusa Kazeem, Oke Oladipupo da kuma Johnson Oluwole bisa laifin satar hular rawanin da sandan sarautan ofishin marigayi Olu na Ogunmakin, Oba Olugbenga Shodiya, wanda ya rasu kimanin watanni biyu da suka gabata.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola ya fitar ya ce Kazeem, Oladipupo da Oluwole a ranar 12 ga watan Oktoba da misalin ƙarfe 2 na safe, sun shiga gidan marigayin suka sace Hular rawanin da sandar sarauta.

Sanarwar ta ce “A ranar 12 ga Oktoba, 2023, an samu bayanan sirri daga fadar Mai Martaba Sarkin Ogunmakin cewa wani mai suna Amusa Kazeem, Oke Oladipupo da Johnson Oluwole sun haɗa baki tare da sace Hula, rawani da sandan Sarauta, watanni bayan rasuwar Sarki Ogunmakin.

KU KUMA KARANTA: Su wa suka sace tirela mai ɗauke da kayan miliyan 550?

“Waɗanda ake zargin sun shiga gidan ne da misalin ƙarfe 2 na safe suka je inda aka ajiye kadarorin marigayi sarki. Mutanen biyu sun ɗauki mabuɗin inda aka ajiye shi a hannun wanda aka ba shi domin ya ajiye kadarorin kuma suka cire Hula, rawani da sandan saurauta na marigayi sarki wani aiki da aka bayyana a matsayin abin ƙyama.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *