Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin, Abba Kabir Yusuf ta ƙaddamar da auren zawarawa 1,800 wanda aka gudanar a Babban Masallacin juma’a na gidan sarkin Kano.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da sauran jiga-jigan jam’iyyar ne, suka jagoranci ɗaurin auren ‘yar gata da aka gudanar a ranar jumu’a a Kano.
KU KUMA KARANTA: Ranar juma’a za a yi auren zawarawa 1,800 a Kano
Haka zalika, an ɗaura auren sauran zawarawan a ƙananan hukumomin Jihar Kano 44, wanda aka gudanar a masallatan Juma’a na shelkwatar ƙananan hukumomin, kamar yadda aka tsara.
Da yake ƙarin haske jim kaɗan da ɗaura auren zawarawan ƙaramar hukumar Ƙunchi, babban limamin ƙaramar hukumar Ƙunchi, Imam Gwani Nazifi Abubakar, ya taya angwaye da amaren murnar sannan ya buƙace su da su zauna da juna cikin aminci da amana.