Wike ya tattauna da makiyaya, da masu sana’ar babura a birnin Abuja

0
207

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin tattaunawa da masu kiwon shanu kafin a fara aiwatar da dokar hana kiwo a tsakiyar birnin Abuja.

Wike ya kuma bayyana shirin samar da wasu hanyoyin sufuri kafin aiwatar da dokar hana zirga-zirgar babura a tsakiyar birnin.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanta wa da manema labarai a ranar Asabar bayan ya duba wasu ayyukan tituna da ke gudana a sassan babban birnin ƙasar.

Ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen gina babban birnin da ‘yan Najeriya za su yi alfahari da shi.

Leave a Reply