Jakadan Faransa a Nijar ya isa gida

0
242

Jakadan Faransa a jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya isa brinin Paris na ƙasar Faransa a jiya Laraba.

Ma’aikatar harkokin waje ta Faransa ce ta tabbatar da hakan, bayan a safiyar Larabar an samu rahoton ficewar ambasadan daga Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar.

Sanarwar ta ce: “Jakadanmu a Nijar ya isa Paris a yau, kamar yadda shugaban ƙasa ya bayar da umarni a ranar Lahadi.”

“Ministan harkokin Turai da ƙasashen ƙetare ne ya tarbe shi domin isar masa da godiya kan yadda shi da tawagarsa suka gudanar da ayyukansu duk da hali na matsi.”

KU KUMA KARANTA: Faransa za ta janye jakadanta a jamhuriyar Nijar

A yau Litinin ne jakadan na Faransa a jamhuriyar Nijar ya bar Yamai, inda ya tashi a jirgin sama daga birnin Ndjamena na ƙasar Chadi zuwa gida.

An kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama bayan da shugabannin mulkin soji na Jamhuriyar Nijar suka umarci jakadan na Faransa da ya fice daga ƙasar bayan ya ƙi amsa gayyatar da suka masa.

Leave a Reply