Gwamnan Ribas ya ba da miliyan 100 ga wanda ya bayyana waɗanda suka kashe DPO a jihar

0
383

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ba da umarnin dakatar da wani sarki har sai baba ta gani dangane da kisan gillar da ‘yan iska suka yi wa jami’in ‘yan sanda na Ahoada, SP Baƙo Angbashim, da “gungun masu laifi.”

A baya dai LIB ta ruwaito cewa an kashe Baƙo ne a yankin Odiemudie da ke ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas (LGA) a jihar a yayin wani artabu da wasu ‘yan ƙungiyar asiri a yankin. 

A wata sanarwa wadda da kansa ya sanya wa hannu, gwamnan ya bayyana baƙin cikinsa kan kashe ɗan sandan.  Gwamna Fubara ya lura cewa manyan waɗanda ake zargin, “Mr.  Gift David Okpara Okpolowu (aka 2-Baba) da dukkan membobin ƙungiyar sa masu aikata laifuka”, an bayyana neman su nan take.  Ya kuma sanar da bayar da tukuicin Naira miliyan 100 ga duk wanda ya samu bayanai masu amfani da ya kai ga kama Okpolowu da gurfanar da shi gaban ƙuliya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Kaduna, sun kashe ‘yan bindiga huɗu, sun kama 13

Ya ƙara da cewa an dakatar da Mai Martaba, Basarake Eze Cassidy Ikegbidi Eze Igbu Akoh II, har sai baba ta gani, saboda laifin da ya yi na bai wa David Gift da ‘yan ƙungiyarsa damar gudanar da ayyukansu cikin walwala, tare da gudanar da ayyukansu na laifuka a yankin da yake da iko.”

Leave a Reply