Gwamnati za ta rufe tashar jirgin saman Legas

0
362

Daga Ibraheem El-Tafseer

Daga ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 2023 za a rufe filin jirgin sauƙa da tashin jiragen saman Murtala Muhammed da ke Legas bayan wani matakin yin wasu gyare-gyare da za a yi a harabar filin jirgin da aka kwashe kusan shekara 43 da ginawa.

Ministan ma’aikatar lura da sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan, inda ya shawarci kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje da su yi amfani da sabuwar harabar da aka kammala kafin a kammala aikin.

Wannan dai ana ganin zai shafi sha’anin sufurin jiragen sama a filin jirgin matuƙar ba an kammala aikin da wuri ba.

A watan Maris ɗin shekara ta 2022 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da buɗe sabon aikin gyaran filin jiragin, amma aikin na fuskantar tafiyar hawainiya.

KU KUMA KARANTA: Lagos za ta ƙaddamar da jirgin ƙasa mai zirga-zirga a cikin gari

A shekrar 2019, tsohon ministan sufurin jirgen sama Hadi Sirika ya fito da shirin rufe filin jirgin saman, sakamakon mummunar lalacewar da ya yi, amma ba a samu damar aiwatar da hakan ba.

Haka ministan ya bayar da sanarwar dakatar da shirin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya har sai ya tattauna da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Festus Kiyamo ya bayyana cewa za a ɗauki matakan gaggawa da suka haɗa da sayo motocin safa-safa domin ɗaukar fasinjoji a filin jirgin.

Ya ce babban abin damuwa ga ‘yan Najeriya da baƙi shi ne yanayin filin jirgi, abin da ya sa za a yi amfani da sabon da wani kamfanin ƙasar Chana ya gina.

Leave a Reply