Akwai barazanar ambaliyar ruwa a jihohi takwas a Najeriya – NEMA

2
307

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ta ce akwai yiyuwar ambaliyar ruwa a jihohin Adamawa, Taraba, Benuwe, Nasarawa, Kogi, Anambra, biyo bayan buɗe ruwa daga madatsar Lagdo da ke ƙasar Kamaru.

Mustapha Ahmed, Darakta Janar na NEMA, wanda ya bayyana hakan a taron ƙungiyar agajin gaggawa ta ƙasa, ranar Laraba a Abuja, ya ce wasu sun haɗa da jihohin Enugu, Edo, Delta, Ribas da Bayelsa.

Ya ce tilas ne jihohin da suke a can ƙasa su fara ɗaukar matakan da suka dace don magance tare da daƙile illolin da ke tafe da ambaliyar ruwa.

A cewarsa, taron ya wajabta ne bisa sanarwar da aka samu daga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, kan yadda aka tsara sakin ruwa daga Dam ɗin Lagdo da ke Kamaru.

Ya ce ƙasar ta fara fitar da ruwa daga madatsar ruwa a kan mita 200 a cikin daƙiƙa ɗaya wanda ya kai kimanin mita 18 na ruwa a kowace rana.

KU KUMA KARANTA: Minista ta yi hasashen ambaliyar ruwa a wasu jihohi

Ya ce sakin na iya haifar da ambaliyar ruwa ga duk jihohin da ke kan gaba a cikin kwanaki da makonni masu zuwa.

“Jihohin da ke gefen kogin Benuwe sune Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Anambara, Enugu, Edo, Delta, Rivers da Bayelsa.

“Bayanan da aka samu daga matakin ruwan kogin Benuwe a tashar auna ma’aunin ruwa ta Najeriya (NIHSA) da ke Makurɗi ya tsaya a mita 8.97 a ranar 25 ga Agusta, 2023 idan aka kwatanta da mita 8.80 a daidai wannan ranar a shekarar 2022.

“Har ila yau, NIHSA ta tanadi cewa tsarin kogin Neja, musamman a Niamey, Jamhuriyar Nijar, ya kasance mai ƙarko a daidai matakin da ya kai mita 4.30.

“Hakazalika, madatsun ruwa na cikin gida da suka haɗa da Kainji, Jebba da Shiroro sun ba da rahoton tsarin gudanar da kwarara,” in ji shi.

Babban daraktan ya ƙara da cewa, gaggawar kwashe ‘yan Najeriya daga al’ummomi daban-daban zuwa wurare masu aminci ya kamata duk masu ruwa da tsaki su aiwatar da su domin daƙile yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a bana.

Sai dai ya yi ƙira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulan su domin hukumar za ta ci gaba da haɗa kai da abokan hulɗar gwamnati wajen samar da tallafi da suka haɗa da abinci da kayan abinci ga mutanen da abin ya shafa a sansanonin ‘yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka karɓi baƙuncinsu.

Tun da farko, Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Hasashen Hukumar NEMA Dakta Onimode Bandele, ya ce an ƙira taron ne domin sabunta bayanai tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban kan batutuwan da suka shafi sakin ruwa daga Dam Lagdo da kuma halin da ake ciki a ƙasar nan.

Ya ce yana da mahimmanci a nemi gudunmawar su mai ma’ana a wasu don tsara hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da za a iya fuskanta, shirya, ragewa da kuma mayar da martani ga matsalolin jin ƙai da sakin ruwa zai iya haifarwa.

A nasa jawabin, Clement Nze, Darakta Janar na NIHSA, ya ce yana da matuƙar muhimmanci a samar da babban shiri a ɓangaren gwamnatin tarayya da na jihohi, musamman a jihohin da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa, dole ne ‘yan ƙasar da suka haɗa da dukkan hukumomi da masu ruwa da tsaki da aka ɗorawa alhakin magance bala’o’i da raguwa, dole ne su ƙara ƙaimi tare da samar da matakan daƙile bala’in ambaliyar ruwa.

2 COMMENTS

Leave a Reply