Lagos za ta ƙaddamar da jirgin ƙasa mai zirga-zirga a cikin gari

2
442

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnatin jihar Lagos ta sanar da cewa rukunin farko na sufurin jirgin ƙasa da zai yi zirga-zirga a cikin birnin Ikko mai taken Blue Rail Line zai fara aiki ranar Litinin 4 ga watan Satumba.

Manajar darakta a hukumar kula da sufuri a ƙwaryar birnin Lagos (LAMATA), Misis Abimbola Akinajo ce ta sanar da haka a tashar jirgin ƙasa ta Marina ranar Laraba, inda ta nunar cewa jirgin farko zai tashi ne da misalin ƙarfe 9 na safe, inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu zai kasance a cikin jirgin tare da sauran fasinjoji daga Marina zuwa tashar Mile 2.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Lagos ta gayyaci ‘yan jarida waɗanda suka zagaya a cikin jirgin ƙasa mai suna Lagosmetro.

Misis Abimbola Akinajo ta bayyana cewa a cikin mako huɗu na farko jirgin ƙasa mai amfani da kwal zai riƙa zirga-zirga tsawon sa’a 12.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan Legas sun kama wasu da ake zargi da ɓarnata titin jirgin kasa

Daga nan kuma sai jirage masu tafiya da lantarki su fara aiki da jigila 76, kuma an yi ƙiyasin cewa jiragen ƙasa za su riƙa ɗaukar fasinjoji tsakanin 150,000 ko 175,000 a kullum yaumin.

Jiragen ƙasa za su riƙa sufuri ne tun daga ƙarfe 5:30 na safe har zuwa ƙarfe 11 na dare.

Misis Abimbola Akinajo ta ce jirgin ƙasan zai riƙa tsayawa ne tsawon minti ɗaya da rabi kawai a kowacce tasha.

2 COMMENTS

Leave a Reply