Sojojin Nijar sun amince su tattauna da ECOWAS

4
244

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wasu bayanai na nuna cewa sojojin na Nijar a yanzu sun ɗan sassauto inda suka nuna alamun yarda su tattauna da ECOWAS.

A baya sojojin sun ƙi bayar da dama ga wata tawaga ta musamman da ECOWAS ta tura Nijar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar domin tattaunawa.

A ranar Asabar majalisar dokokin ƙungiyar ta ƙasashen Afirka ta Yamma ta ce za ta tura wani kwamiti babban birnin Nijar ɗin Niamey.

Sai dai kuma ba ta sanar da ainihin lokacin da za ta tura kwamitin ba.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar ECOWAS game da ɗaukar matakin soji

Haka kuma a ranar Litinin ɗin ne kwamitin tsaro na ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU, kasashe 55 zai gana domin tattauna yanayin na Nijar.

Ana ganin wannan wata alama ce ta nuna damuwa kan wannan juyin mulki, wanda ya kasance na bakwai a tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a cikin shekara uku.

Wani abu da ke ɗaukar hankali a kan halin da nahiyar ke ciki dangane da juyin mulkin da ake samu shi ne ba wai makomar Nijar ba kaɗai, wadda kasa ce mai arziƙin sinadarin yureniyom, da kuma kasancewarta kawar ƙasashen Yamma a yaƙi da masu iƙirarin jihadi, akwai fargabar gogayya da ake samu da sauran manyan ƙasashen duniya abokan hammayyar Yamma, domin samun tasiri a nahiyar.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka da majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Tarayyar Turai dukkaninsu sun mara baya ga ECOWAS a kan duk matakin da za ta ɗauka na mayar da dimukuraɗiyya da kuma Shugaba Bazoum kan mulki.

Ƙungiyoyin har ma da Amurka sun nuna damuwa game da lafiyar shugaban kan halin da aka ce yana ciki, saboda yadda yake tsare.

A ranar Asabar ne wata tawaga ta shugabannin addinin Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Bala Lau, na ƙungiyar Izala ta je Yamai domin tattauna batun na Nijar.

Tawagar wadda ta samu ganawa da sabon Firaministan da sojoji suka naɗa, Ali Mahaman Lamine Zeine, ta kuma samu ganawa da jagoran juyin mulkin wanda ya naɗa kansa sabon shugaban ƙasa Janar Abdourahamen Tchinai.

Bayanai sun nuna cewa tawagar ta shugaban na ƙungiyar Izala ta je Nijar ɗin ne bisa izinin ƙungiyar ECOWAS da kuma shugabanta wanda kuma shi ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, domin kwantar da hankali ganin yadda lamarin ke neman haifar da tashin-tashina saboda matakin soji da ECOWAS ke cewa za ta ɗauka.

Ganin yadda matakin da ECOWAS ta ɗauka na sanya wasu jerin takunkumai a kan Nijar ɗin na neman haifar da tsama tsakanin ƙasashen biyu, malaman sun nuna wa sojojin cewa wannan mataki ne na ƙungiya amma ba Najeriya ba, kamar yadda bayanai suka nuna.

A makon da ya gabata ne Sheikh Bala Lau da ‘yan tawagar tasa suka gana da Shugaba Tinubu a Abuja, inda bayanai suka ce a wannan zama ne aka tsara zuwa ganawa da shugabannin juyin mulkin na Nijar.

ECOWAS ta jaddada cewa har yanzu dukkanin wata ƙofa ta sasanta rikicin na Nijar a buɗe take, kuma matakin soji zai ci gaba da kasancewa zaɓi na ƙarshe idan komai ya ci tura.

Ministan harkokin waje na gwamnatin Nijar da sojojin suka hamɓarar, Hassoumi Massaoudou, yace matakin soji da ECOWAS ke cewa za ta ɗauka a kan masu juyin mulkin ba yaƙi ne a kan Nijar da ‘yan ƙasar ba, matakin tabbatar da doka ne a kan waɗanda ya ƙira masu garkuwa da mutane da masu taimaka musu.

4 COMMENTS

Leave a Reply