Kwalekwale ya nutse da ‘yan mata tara a Jega ta jihar Kebbi

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Jega a jihar Kebbi na cewa ana fargaban wasu ‘yan mata tara sun nutse a cikin ruwa sakamakon haɗarin kwalekwale.

Majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne a Mashayar ɗan kale a mazaɓar kokani Ward da ke garin Jega, inda ‘yan mata daga garin Unguwar Kurya  su tara (9) suka nutse.

Majiyar ta ce Sarkin Ruwan Jega ƙarƙashin Masarautar Jega sun jagoranci ƙungiyar matsunta da masu lalaɓe domin ceto waɗannan bayin Allah.

Ana kyautata zaton an ceto ‘yan mata guda biyu, ɗaya da ranta aka garzaya da ita Asibi. Ɗaya kuma an ceto ta ba ta da rai. An miƙa ta ga ‘yan uwanta.

KU KUMA KARANTA: Mutane huɗu sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Yanzu haka ana kan neman sauran ‘yan matan guda bakwai a cikin ruwan.

Ƙoƙarin mu na jin ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Jega ta wayar salula ya ci tura, domin dai bai amsa ƙiraye-ƙiraye da muka yi masa a wayarsa ta salula ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *