Idan da gaske an karɓo kuɗaɗen da Abacha ya sata, to a gaya wa duniya adadin da kuma abin da aka yi da su – Dakta Hassan Gimba a hirarsa da RFI Hausa

0
519

Daga Ibraheem El-Tafseer

Fitaccen ɗan jaridar nan kuma marubuci. Mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba ne ya bayyana haka a hirarsa da sashen Hausa na gidaan ‘Radio France International’ (RFI Hausa) a ranar Laraba.


Gidan Rediyon sun fara da tambayarsa ne akan hukuncin da kotu ta zartar kan ƙarar da ƙungiyar SERAP ta shigar na sanin haƙiƙanin kuɗin da tsohon shugaban Najeriya, Janaral Sani Abacha ya sata, zunzurutun kuɗi har dala biliyan biyar na Amurka. Kotun ta bawa gwamnatin Najeriya wa’adin kwanaki bakwai don ta yiwa duniya cikakken bayani akan wannan kuɗi.

Dakta Hassan Gimba shi ne ya yi fashin baƙi kan wannan hukunci, ga abin da yake cewa a tattaunawarsa da RFI Hausa;


Dakta Hassan Gimba – Shi maganar kuɗin da ake cewa Abacha ya sata, sai ya zama kamar wani ƙanzon Kurege. Kamar azancin ko karin maganar (quotations) na Robert Mugabe, mutum sai ya yi shaci faɗi, ya kawo wata magana, sai ya ce Robert Mugabe ne ya faɗa. Abu kaɗan, bini-bini sai a ce kuɗin da Abacha ya sata. An yi ta faɗin haka, jama’a ba za su ga kuɗi ba, ba za su ga abin da aka yi da kuɗi ba. An ce an karɓo kuɗi, to ina kuɗin? Ina ayyukan da aka yi da su?

RFI Hausa – Kana ga an yi amfani da kuɗin da ake cewa an karɓo ta hanyar da ta dace?

Dakta Hassan Gimba – Yanzu duk cikinsu babu wanda za ka tsare, ka ce ina abin da aka yi da kuɗin da ake cewa an dawo da su na Abacha ɗin ya nuna maka. Shi ya sa da SERAP ɗin ta rubutawa ma’aikatar kuɗi akan ku yi mana bayani na kuɗaɗen da Abacha ɗin ya sata duka-duka nawa ne? Sannan kuɗaɗen da aka karɓo ɗin duka-duka nawa ne? Kuma ku nuna mana me aka yi da kuɗaɗen. Ai ma’aikatar kuɗin sai suka ƙi. Idan da gaskiya su faɗa mana.

Shi ya sa sai SERAP ɗin ta je kotu, ta ce a ce musu su faɗa. Sai ma’aikatar kuɗin ta je kotu tana kare wa, wai ba za su faɗa ba, domin ba su san adadin kuɗin ba, wai ba su da ‘record’. Yaya za a yi kuɗi ya shigo Najeriya a ce ma’aikatar kuɗi ba ta da ‘record’? Wannan ya nuna akwai wani abu a ƙasa da ba a so duniya ta sani. Shi ya sa Alƙalin ma ta ce dole su faɗa. Sai suke cewa wai me ya shafi SERAP a ciki. Wai SERAP ɗin ba ta nuna tana so ta san abin ba. Ba so su sani kuma za su rubuta su ce a gaya musu? Shi ne kotu ta ce lallai su fito su faɗa wa duniya.
Tun daga gwamnatin farko har ta Buhari da ake cewa mai gaskiya, kullum wai karɓar kuɗin Abacha suke yi to a nuna mana me aka yi da kuɗin.

RFI Hausa – Ba Abacha kaɗai ne ya yi mulki a Najeriya ba, me ya sa ba a bibiyar sauran shugabannin?

KU KUMA KARANTA: Burina a tuna dani a marabucin da ke nusar da shugabannin – Hassan Gimba burin a tuna ni a marubucin dake nusar da shugabanni – Gimba

Dakta Hassan Gimba – Shi ne abin da Bahaushe ke cewa ‘mutuwa mai tonon asiri’. Amma shi Abacha an san ƙullalliyar da ke tsakaninsa da Obasanjo ko? Obasanjo mutum ne da ba ya yafiya. Yana ga Abacha ya kama shi. To me zai yi ya tozarta shi, ya lalata shi, ya ɓata masa suna har duniya ta naɗe. Shi ya sa ya ƙirƙiro ya ce Abacha ya yi sata. To mun yarda ya yi sata ɗin, to ina kuɗin? A gaya wa duniya nawa ne ya sata? Kuma da kuka ce an karɓo kuɗin, to ina kuɗin yake? kuma me aka yi da kuɗin? Wajen dala biliyan biyar, ya isa ya canza Najeriya kaf, a ce ko ba mu kamo Dubai ba, muna jin, ƙamshin dubai. Ba gaskiya a zancen sam.

RFI Hausa – Wane ƙalubale ne ke gaban sabon shugaban ƙasa game da wannan hukunci na kotu kan wannan kuɗi?

Dakta Hassan Gimba – Tana da abu biyu, don yanzu ta fara. Kuma ita kanta cin zaɓenta yana gaban kotu, don ba Nijeriya kaɗai ba, sun yi magana akan yadda ta zaɓe. Dole ne su yi ƙoƙori su nuna wa duniya suna so su yi gaskiya. Kuma tun da haka ne, sai nuna wa duniya duk abin da kotu ta ce za su bi. Idan gwamnatin da ta shuɗe ne, ina tabbatar maka da yanzu sun ɗqukaka ƙara. To wannan gwamnatin idan ita ma ta ɗaukaka ƙara, to mun san akwai wani abu. Amma idan suna da gaskiya babu batun ɗaukaka ƙara, sai su kira mutanen gwamnatin da ta shuɗe, ku zo ku gaya mana, ina kuɗaɗen, me aka da su? To sai su gaya wa duniya. Amma idan suka fara ɓoye-ɓoye to mun san akwai wani abu.

Ga yadda hiran su ta kasance

Leave a Reply