Kotu ta umurci sojojin Najeriya da su biya 260,000 ga al’ummar Jaji

0
401

A ranar Alhamis ne wata babbar kotun jihar Kaduna ta umurci sojojin Najeriya da su biya naira 260,000 ga al’ummar ƙaramar hukumar Jaji.

Mai shari’a Hannatu Balogun ta umurci rundunar da ta biya kowane membobi 260 kuɗin naira 1,000 sannan kuma, ta bayar da shaidar biyansu kafin ranar 10 ga watan Yuli.

Ta kuma umurci sojojin da su baiwa al’ummar yankin damar shiga gonakinsu.

Tun da farko, Lauyan masu shigar da ƙara, Kimi Livingston ya shigar da ƙara a gaban babban kwamandan rundunar, 1 Division da wasu manyan hafsoshi.

Sun yi zargin cewa sojojin sun ƙi bin umarnin kotu ne wanda ya dakatar da gina shingen da aka yi wa barikin Jaji.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun hanyoyin tace mai 57, sun kama 16

Har ila yau, sun yi zargin cewa sojojin sun hana masu shigar da ƙaran damar shiga gonakinsu da ƙauyuka da al’ummominsu a lokacin da ake ci gaba da shari’ar.

Waɗanda ake ƙara ba su a kotu amma sun aika da wasiƙa cewa an mayar da jami’an da ke ofisoshin zuwa wasu wurare.

Alƙalin ya ƙi karɓar wasiƙar. Lauyan wanda ake ƙara, Aliyu Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa zai tabbatar da cewa jami’an sun kasance a kotu da kansu kafin ranar 10 ga watan Yuli.

Ya kuma musanta zargin hana al’umma shiga gonakinsu.

A ranar Nuwamba 2020 ne al’ummomin da suka karɓi baƙuncinsu a cikin ƙaramar Hukumar Soja ta Jaji, sun kai ƙarar sojoji zuwa Kotun ƙoli ta Jihar, bisa zargin yin katsalandan da ƙasar kakanninsu.

Al’ummomin da suka haɗa da Wusono, Ungwan Auta, Labar, da Ungwan Alhassan, sun kasance a gaban kotu saboda sojoji sun fara killace al’ummar ƙaramar hukumar a yayin da ake ci gaba da sasantawa.

Leave a Reply