Basarake ya ƙona magidanci, ya mutu har lahira a Yobe

0
698

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a ranar Asabar ɗin da ta gabata ta ce ta kama wani basarake da ‘ya’yansa biyu kan kisan wani Goni Waje a ƙauyen Dako Kangarwa da ke ƙaramar hukumar Yunusari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin Jalomi, Ciroma da Bulama.

Mista Dungus, ya ce kisan ya auku ne a ranar 7 ga watan Yuni bayan mutanen uku sun zargi Waje da yin lalata da matar Bulama, hakimin yankin kuma mahaifin Jalomi da Ciroma.

“Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, an yi wa mamacin yankan rago tare da kone shi ƙurmus daga hannun Alhaji Jalomi da Ciroma.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

“Kamar yadda aka ruwaito, lamarin ya fara ne da faɗa da ya kai ga mamacin ya yi amfani da wuƙa wajen raunata mahaifin waɗanda ake zargin,” in ji Mista Abdulkarim.

Ya ƙara da cewa daga baya Bulama ya umurci ‘ya’yansa da su bi Waje, inda suka shi ƙona shi har lahira.

Mista Abdulkarim ya ce waɗanda ake zargin uku sun miƙa kansu ga ofishin ‘yan sanda na yankin Yunusari bayan faruwar lamarin.

“Yayin da Bulama ke neman hanyoyin da zai yi wa kansa magani daga raunin da ya samu, ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya sa ‘yan sanda su gudanar da bincike.

“Wanda aka kashe ya bayyana a matsayin wanda ake tuhuma, wanda hakan ya sa aka kama shi a ofishin ‘yan sanda na Yunusari “

Daga baya, waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin sun kai rahoton kansu ga sashin Yunusari bayan kama mahaifinsu,” in ji shi.

Mista Abdulkarim ya ce an miƙa mutanen uku zuwa sashin binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.

Kakakin ya ce an ajiye gawar Mista Waje a asibitin ƙwararru da ke Damaturu.

Leave a Reply