Ko ka san amfanin jigida a jikin mace?

1
934

Jigida wani abu ne da ake sanyawa a ƙugu wadda mata ke amfani da shi, kamar sauran ababen kwalliyar gargajiya irin su; Agogo, Awarwaro, Sarƙar Wuya, Zobe, da ‘yan kunne da mata ke sanyawa a jikinsu. Kwalliyar ƙugu dai, mata ne ke yi domin kwalliya.

A zamanin baya, matan nahiyar Afirka suna sanya Jigida ne a matsayin alamar mace da kuma jan hankali.

Wasu kuma sun yi imanin sanya Jigida na taimaka musu wajen lura da nauyinsu.

KU KUMA KARANTA: Mace ɗaya ‘tilo’ mai gyaran wayar salula a jihar Borno

A wasu yankunan ana haɗa jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen ɓoye, wato aljanu.

Wani jigidan akan haɗa da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman ƙananan yara.

Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun sauƙin naƙuda a lokaci haihuwa.

Akwai yaƙinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage ƙiba musamman ga mata masu tumbi ko ƙaton ciki.

Jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman ƙugu wato ‘Hips’ a Turance, da kuma samun farin jini cikin mutane.

Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace.

1 COMMENT

Leave a Reply