Gwamnatin Zamfara ta bai wa Matawalle wa’adin mayar da motocin alfarma na biliyoyin nairori

2
245

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa tsohon gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle wa’adin kwanaki biyar da ya bayar da bahasi kan motocin alfarma na biliyoyin nairori da aka sayo daga susun gwamnatin jihar, kuma suka yi ɓatan-dabo.

A cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai Sulaiman Bala Idris ya fitar ya ce sabuwar gwamnati ta samu hujja da alaƙaluman kuɗin da aka ware wajen sayo wasu manyan motocin alfarma.

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta samu hujja mai ƙarfi da ke nuna cewa tsohon gwamnan ya ware biliyoyin nairori wajen sayo manyan motocin alfarma da gwamnati za ta yi amfani da su.

KU KUMA KARANTA: Matawalle ya wawure motoci 17, injinan gas, da na’urorin talabijin na jami’an gwamnati – Gwamna Dauda

Sai dai sanarwar ta ce sabuwar gwamnati ba ta samu ko da mota guda cikin motocin da tsohuwar gwamnatin ta ce ta sayo ba, kamar yadda bayanai suka nuna.

A baya-bayan nan dai tsohon gwamnan na ta samun taƙun-saƙa da hukumar yaƙi da cin hanci da rasha EFCC bayan da ya zargi shugaban hukumar Abdurrasheed Bawa da aikata almundaha iri-iri.

A cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar cikin makonni da suka gabata, ta ce tana bincikar gwamna Matawalle ne kan zargin karkatar da Naira biliyan 70, da bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba.

“Kuɗin wanda aka samu a matsayin bashi daga wani banki domin aiwatar da ayyuka a sassan ƙananan hukumomin jihar, ana zargin gwamnan ya karkatar da shi ne,” kamar yadda sanarwar EFCCn ta bayyana.

A martanin da ya mayar tsohon gwamnan ya ƙalubalanci Bawa da ya sauka daga kan kujerarsa ya bayar da damar a bincike shi ya ga irin abubuwan da za a bankaɗo.

Cikin wata hira da ya yi da BBC Matawalle ya ce “Bincike gaskiya ne, ba a hana a yi bincike ba, amma kuma ya kamata binciken ya zamo na kowa da kowa, don bai kamata a ce komai sai dai a ambaci gwamna ba, ai ba gwamna ne kaɗai ke da asusun ajiya ba.”

Ya ce, “Kamar yadda shugaban EFCC ya ce ya tanadi takardu na gwamnoni, to muna so ya nuna wa duniya takardu na waɗanda yake aiki tare da su, sannan shi kansa ya kamata ya rubuta wa kansa takarda don a bincike shi saboda akwai zarge-zarge masu ɗimbin yawa a kansa.”

2 COMMENTS

Leave a Reply