An tsaurara tsaro a wajen ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Adamawa

An tsaurara tsaro a lokacin da jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta na ƙasa (INEC) suka sake taro a cibiyar tattara sakamakon zaɓe a jihar Adamawa

Jami’an tsaro sun isa cibiyar tattara sakamakon zaɓen jihar da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa yayin da jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ke ci gaba da zama.

‘News Point’ Nigeria ta ruwaito cewa, an ga sakataren hukumar zaɓe ta INEC a jihar, Adamu Gujungu, wanda aka ba da umarnin ya maye gurbin kwamishinan zaɓe Hudu Yunusa Ari a wurin tattara sakamakon zaɓen.

KU KUMA KARANTA: Ta maka INEC da PDP a kotu kan zargin ayyana ta a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamnan Adamawa – Binani

Ana sa ran kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye a wurin tattara sakamakon zaɓen.

A ranar Lahadi ne INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa da aka gudanar a ranar Asabar bayan Ari ya bayyana Aisha Binani Ɗahiru na jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen tsakaninta da gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Nan take INEC ta gayyaci Ari zuwa Abuja tare da ayyana sanarwar sa a matsayin shela marar inganci da kuma ƙwace ikon jami’an tattara bayanai da na dawo da su.

Alƙalin zaɓen ya kuma ce zai rubutawa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba domin ya binciki Ari. Kafin a dakatar da aikin tattara sakamakon a daren Asabar, an sanar da sakamakon ƙananan hukumomi 10 – kuma Binani tana bin Fintiri.

Da misalin ƙarfe 11 na safiyar Lahadi ne ake sa ran fara tattara sakamakon sauran ƙananan hukumomi 10 da suka rage, kuma Mele Lamido, jami’in zaɓen gwamnan Adamawa, bai halarci ba lokacin da Ari ya bayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaɓen.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada, Lamiɗo ne jami’in da ya dace ya bayyana wanda ya lashe zaɓen.


Comments

One response to “An tsaurara tsaro a wajen ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Adamawa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An tsaurara tsaro a wajen ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Adamawa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *