Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, ya lashe kujerarsa

1
480

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen mazaɓar tarayya ta Tudunwada/Doguwa a jihar Kano.

Alhassan Doguwa ya zama wanda ya yi nasara a zaɓen da aka ƙarasa a ranar Asabar a yankin.

Jami’in zaɓe na INEC, Farfesa Sani Ibrahim ne ya sanar da sakamakon, inda ya ce jam’iyyar APC, ɗan takararta ya samu ƙuri’u 41,573.

Babban abokin hamayyarsa kuma ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Yushau Salisu, ya samu ƙuri’u 34,831, yayin da jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 211.

KU KUMA KARANTA: Za a sake zaɓe a mazaɓar Ado Doguwa

Rijistar ta nuna cewa mutane 227, 912 ne aka yi wa rajista, sannan 80,933 suka samu tantancewa.

Amma bayan atisayen na ranar Asabar, jimillar ƙuri’un da aka kaɗa ya kai 79,705; masu inganci 78,788, kuma ƙuri’un da aka ƙi amincewa sun kai 917.

1 COMMENT

Leave a Reply