Yadda ‘yan sanda suka kama gungun ɓarayin waya a Alaba-rago da Ajegunle a jihar Lagos

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wasu ‘yan fashi da makami guda shida ‘yan gungun ’yan daba daban-daban da suka yi ƙaurin suna wajen ƙwace dukiyar mutanen da ba su ji ba gani ba a unguwar Ajegunle da Alaba-Rago a jihar Legas.

A cewar mai magana da yawu rundunar ‘yan sandan jihar Legas SP Benjamin Hundeyin kamen ya biyo bayan gudanar da bincike cikin gaggawa kan rahotannin ayyukan ‘yan fashin a yankunan.

Ya ce waɗanda ake zargin suna haɗarda Chukwuemeka Emmanuel mai shekaru 21 da Chukwuebuka Innocent mai shekaru 24, sai Umaru Isah, mai shekaru 21 da Emmanuel Ita mai shekaru 19, da kuma Olayitan Ayinde mai shekaru 18, sai Moshood Ayinde ‘mai shekaru 25, an kuma kama su ne a yankuna daban-daban na jihar, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin damke wasu ‘yan ƙungiyar da suka tsere da kuma ƙwato makamansu.

KU KUMA KARANTA: Masu garkuwa sun sace matasa 21, har da budurwa da ke aikin tara kuɗin aurenta

Ya ƙara da cewa an samu nasarar ƙwato babur ɗaya ƙirar TVS da ba a yi rajistar sa ba, da bindiga guda ɗaya ƙirar gida, da wayar Infinix Note 7 ɗaya da kuma Iphone 7 daya daga hannun waɗanda ake zargin, za kuma a gurfanar dasu a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Legas, CP Idowu Owohunwa, ya buƙaci al’ummar jihar Legas da su gaggauta sanar da ‘yan sanda abubuwan da ke faruwa a yankunansu, al’amuran da suka shafi waɗanda ake zargi da aikata laifuka domin ƙara baiwa ‘yan sanda damar kawar da ɓatagari a jihar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *