Sakamakon zaɓe: ‘Yan Sanda sun gargaɗi ‘yan siyasa

0
367

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jiya ta gargaɗi ‘yan siyasa da su ƙaurace wa matsin lambar da ba dole ba a kan hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta.

Rundunar ta ce an yi nuni da cewa, ana aiki tuƙuru don shirin gaggauta kammala tattara sakamakon babban zaɓen na ranar Asabar da kuma bayyana wanda ya yi nasara.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, a cikin wata sanarwa, ya gargaɗi ‘yan siyasa game da zafafa harkokin siyasa.

Ya kuma ɓukaci ɗaukacin ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen na ranar Asabar da su gargaɗi magoya bayansu game da tunzura jama’a. Ya ce ‘yan sanda ba za su yi maraba da kuma zafafa ayyukan siyasa da ke tasowa ba a tsakanin masu zaɓe da sauran jama’a.

KU KUMA KARANTA: Zaɓen 2023: A daina yaɗa sakamakon zaɓe na ƙarya, in ji ‘yan sanda

Ya ce rundunar ‘yan sandan ta yaba wa jama’a da masu zaɓe bisa haƙuri da suka nuna har zuwa yanzu da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu na halal a faɗin ƙasar nan.

Ya ce rundunar ta kuma ƙarfafa gwiwar ‘yan takarar shugaban ƙasa da su gargadi magoya bayansu da su kiyaye ƙa’idojin yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu kwanan nan domin gudanar da babban zaɓen ƙasar cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply