Yadda ƙarancin naira ya haddasa rikici a Ogun

7
376

Tsoro ya dabaibaye mazauna garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, da ‘yan kasuwa, yayin da wasu fusatattun matasa suka gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na babban birnin jihar.

Rahotanni sun ce an fara zanga-zangar ne a yankin Asero a Abeokuta, a ranar talata, da wasu abokan hulɗar bankin GTBank suka yi kan rashin samun sabbin takardun kuɗi na Naira daga bankin.

Masu zanga-zangar da suka yi tashe-tashen hankula a kan tituna sun tare hanyar da ta nufi Adatan da Osiele zuwa Ibadan a yayin zanga-zangar.

Haka kuma zanga-zangar ta bazu zuwa Adatan, Sapon, Oke-Ilewo, Lafenwa da dai sauransu, inda jama’a suka yi ta rataye ganye a jikin ababan hawansu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya yi gaggawar garzayawa wurin da lamarin ya faru domin kwantar da hankulan da ya tilastawa jami’an bankin dakatar da ayyukansu.

KU KUMA KARANTA: CBN zai hukunta duk bankunan da ke ɓoye sabbin kuɗi

An kuma ɗauki matakin ne a lokaci guda yayin da wasu matasa da suka fusata suka je Sapon, Lafenwa, Adatan, Gbonagun Obantoko inda suka gudanar da zanga-zangar.

Wani banki a Sapon ya dakatar da aikinsa ba tare da bata lokaci ba don gudun kada a kai masa hari yayin da bankunan Oke-Ilewo da Panseke suma suka rufe ofisoshinsu kafin fusatattun matasan su far musu.

An ga wasu ma’aikatan bankunan a Oke-Ilewo da Panseke sun fice daga harabar da gudu, daga bisani matasan sun isa Oke-Ilewo inda suka lalata duk wasu kayan ‘yan siyasa da suka rataya akan fitilun kan titi.

Matasan da ke tafiya a kan babura sun kuma tare hanyar Lalubu a yayin zanga-zangar, inda suka hana zirga-zirgar ababen hawa, sun yi ta harbe-harbe a wasu wurare yayin da ba a ga ’yan sanda ba sai bayan fusatattun matasan sun bar wurin.

Haka kuma wasu masu zanga-zangar sun kai farmaki wani reshen bankin First Bank da ke Lafenwa a Abeokuta inda suka lalata na’urar tantance motoci da ke bankin.

An kuma bayyana cewa an rufe makarantu sakamakon ruɗanin da aka samu yayin da aka kai hari wata makarantar sakandare dake Gbonagun, Obantoko.

Wani malami a makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an jefa barkonon tsohuwa cikin harabar makarantar, kuma malaman sun yi gaggawar kwashe daliban zuwa wuri mafi aminci.

Tarzomar ta garin Abeokuta tayi salwantar mutuwar mutum guda, wanda bidiyonsa yayi ta kareɗe shafin sada zumunta inda aka ganshi an harve shi da bindiga ya riqe wajen a gefen cikinsa a lokacin da yake qoqarin tsallaka kwata amma ya faɗa cikinta.

7 COMMENTS

Leave a Reply