DSS
‘Jami’an DSS ba suyi kutse a CBN ba’
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/01/IMG-20230116-WA0020.jpg)
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi martani kan labarin nan da ya bazu a ranar Litinin cewa jami’anta sun yi kutse a hedkwatar babban bankin Najeriya wato CBN.
A sanarwar da mai magana da yawu hukumar Peter Afunaya ya fitar a ranar ta Litinin ya ce labarin karya da ake yaɗaawa cewa jami’anta sun mamaye babban bankin Najeriya tare da kama gwamnansa, a ranar Litinin 16/1/23.
“Wannan labari ba gaskiya ba ne, kuma yaudara ce” in ji shi.
KU KUMA KARANTA;Za a daina amfani da tsoffin kuɗaɗen Najeriya a watan Janairu 2023
DSS
DSS ta sako wacce ta soki gwamnatin Kaduna a Facebook
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/04/Screenshot_20230112-150141.jpg)
An sako Aisha Galadima, wacce take kare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka kama don yin bincike.
Aminiya ta ruwaito yadda aka damƙe ’yar Jam’iyyar APC a Kaduna bisa wani rubutu da ta yi a Facebook kan Gwamna Uba Sani.
A cewar majiyoyi, Aisha Galadima ta soki kalaman Gwamna Uba Sani na ƙarshe a kan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.
Wata ƙwabciyarta ta ce, an kama ta ne a unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi da yamma, kuma wata abokiyarta ta bayyana cewa wayar Aisha a kashe take bayan tsare ta da aka yi.
Sai dai babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya ce ba shi da masaniyar kama ta.
“Ban san an kama wata mata da ta rubuta munanan kalamai a kan Gwamna ba. Amma kuna iya mika tambayoyinku ga hukumar DSS ba gwamnatin jihar Kaduna ba,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: El-Rufai ya bar wa jihar Kaduna ɗimbim bashi – Gwamnan Uba Sani
An sake ta ne bayan da ta kai kusan awa 24 a hannun hukuma.
Da aka tuntuɓi Aisha, ta tabbatar da sakin nata, inda ta ce jami’an hukumar sun tursasa tare da dukan ta.
“Ina cikin ɗakina zan yi wanka sai suka shigo suka ja ni. Na ga motar su ƙirar Hilux hudu a wajen gidan. Suka tura ni ciki suka wuce,” in ji ta.
A cewarta, (DSS) sun zarge ta da yin wani rubutu a kan gwamnan a watan Fabrairu.
DSS
DSS sun cafke shugaban ƙungiyar Miyatti Allah
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/01/Screenshot_20240124-085236_1.jpg)
Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a jihar Nasarawa.
Wasu shugabannin ƙungiyarsa ta Kautal Hore kuma makusanta sun tabbatar da batun kama Bodejo a jiya Talata.
Sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.
Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.
A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani.
KU KUMA KARANTA: An ɗaure Sarkin Fulani da ‘yan uwansa 2 kan garkuwa da mutane
Bayanai na cewa jami’an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa ƙirƙiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.
DSS
DSS ta ce shugabanta bai sace kuɗin tallafi na ma’aikatan hukumar ba
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2023/12/Screenshot_20231203-120503_1.jpg)
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya DSS ta musanta zarge-zargen da ake yi kan cewa babban daraktan hukumar Magaji Yusuf Bichi ya yi sama da faɗi da kuɗin tallafi na ma’aikatan hukumar.
Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ne ya fitar da sanarwar inda ya musanta zargin da wani Jackson Ude ya yi a shafin X wanda ya yi zargin shugaban DSS din da kwashe kuɗin.
Afunanya ya tabbatar da cewa babu wasu kuɗi da aka bai wa hukumar a halin yanzu domin ma’aikata kuma da zarar an fitar da waɗannan kuɗaɗe za a bai wa ma’aikatan hakkinsu.
“Hukumar tana son sanar da cewa zarge-zargen da ake yi ba gaskiya bane. Hukumar na son tabbatar da cewa daraktan hukumar ko wani mai aiki da umarnin shi, babu a cikinsu wanda ya sace kuɗin tallafin da aka bai wa ma’aikata.
KU KUMA KARANTA: Sojoji da DSS sun daƙile yunkurin Boko Haram na kai hari a Kano
“Babu wani tallafi da aka bai wa hukumar kuma da zarar an bayar da shi, za a bai wa ma’aikatan hakkinsu,” in ji sanarwar.
Hukumar ta DSS ta buƙaci jama’a su yi watsi da ƙarerayin da ake yaɗawa waɗanda ke kawo rabuwar kai da kuma rikici.
Haka kuma hukumar ta tabbatar da cewa daraktan na DSS zai ɗauki matakai na shari’a dangane da lamarin.
-
Kotu1 year ago
Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida
-
Labarai9 months ago
Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum
-
Ƙasashen Waje1 year ago
Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar
-
Labarai1 year ago
‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano
Pingback: CBN zai hukunta duk bankunan da ke ɓoye sabbin kuɗi | Neptune Prime Hausa