Yadda aka kama matashin mai damfarar masu POS

1
303

Wani matashin mai shekaru 26 mai suna Emmanuel Okorafor da ake zargi da da laifin zamba cikin aminci tare da damfara masu POS ya shiga komar ‘yan sanda.

Matashin ya furta cewa ya fara damfarar masu POS ne makonni uku da suka gabata inda yayi ta damfararsu maƙudan kuɗaɗe.

Ya ce yakan nemi ya cire kuɗi adadin naira dubu hamsin zuwa sama, da zarar ya faɗa masu sun rubuta, idan sun miƙo masa na’urar ya sanya PIN zai ya yi sauri ya cire sufuli biyu, misali idan dubu hamsin da biyu ne sai ya mayar dubu biyar da ɗari biyu ta yadda za a cire dubu biyar da ɗari biyu a bankinsa amma sau a bashi naira dubu hamsin da biyu, wato daga (N52,000:00). zuwa (N5,200:00).

Da wannan ne ma’aikatan za su biya shi N52,000:00 yayin da ake cire masa N5,200:00.

A cikin ikirarin nasa, ya ce yayi irin wannan zamba a wuraren POS biyar a ranar Alhamis a kusa da unguwar Ogudu da Ojota a Legas kafin rundunar ‘yan sandan RRS su kama shi da yammacin ranar Juma’a.

Kamar yadda ya faru a jiya, ma’aikatan POS guda uku sun ce ya yi musu wannan dabara da ATM dinsa.

KU KUMA KARANTA:Wasu ‘yan damfara da suka tursasa wata mace cire kuɗi a banki sun shiga hannu

Rundunar ‘yan sanda ta ce wasu daga masu POS din sun yi tuhuma tare da korar da yawa daga cikin yaransu da ke masu hidima domin sun zata yaran ne je sace masu kuɗi.

Bincike ya nuna cewa matashin Emmanuel Okorafor ya yi amfani da na’urar ATM ne wajen karɓar maƙudan kuɗaɗe daga Naira 52,000 zuwa N5500 a wuraren POS da dama.

1 COMMENT

Leave a Reply