Dalilin nasarar aurena- Fati Ladan

0
288

Tsohuwar sarauniyar Kannywood kuma tsohuwar jarumar fim, Fati Ladan wadda ta yi bikin cika shekaru 9 da aure ta bayyana dalilan da suka kai ga samun nasarar auren ta, ta kuma shawarci sauran ma’aurata da su ga nasarar auren ta, a matsayin misali su ma su samu nasarar rayuwar iyali.

Fati Ladan ta jaddada cewa tun farko ta damu da rashin haihuwa na wani lokaci amma da yake Allah ya kaita mijinta da iyalansa sun ci gaba da yi mata nasiha da ta yi haƙuri da rokon Allah, domin Ubangiji shi kaɗai yake da iko, wannan nasihar ta yi mata tasiri, domin a yanzu Fati ta haifawa mijinta Yarima Shettima ‘ya’ya biyu.

KU KUMA KARANTA:Bana cajin ƙasa da naira miliyan ɗaya a kowane fim- Hadiza Gabon

Hakazalika Fati ta bayyana cewa, a bana saɓanin shekarun baya, ta yanke shawarar gayyato makwabtanta ne kawai, danginta da matan Yakubu Lere da Adam Zango waɗanda suka halarci bikin wanda aka shirya a gidansu na Kanta Road da ke Kaduna a kan titin Yerima Shettima.

“Ina so in shaida maku cewa mijina mutumin kirki ne,kuma magidanci na gari, tsawon shekaru tara da muka yi tare muna yi kuskure, amma a ko yaushe ya tsaya tsayin daka kuma tare da tabbatar da nasarar aurenmu, ina godiya a gare shi bisa fahimtarsa, shi ya sa a duk lokacin da mu matansa muke addu’a biyu muke yi, muna addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya buɗa masa kofofinsa, a matsayinsa na Shugaban Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa, aikinsa na da hadari a mafi yawan lokuta,kullum yana cikin tafiya amma mun saba da haka” in ji Fati Kadan.

Yerima Shettima, shugaban matasa mai fafutukar kare hakkin ɗan Adam kuma shugaban al’umma shi ma a daidai wannan lokaci ya bayyana iyalansa a matsayin masu fahimtar juna kuma ya yabawa Fati da matarsa ​​ta biyu a matsayin iyali na ban mamaki, tsawon shekarun da suka gabata sun zama kamar masu ba shi shawara domin babu wanda ya kamace shi face suna yin iya ƙoƙarinsu don ganin ya tafiyar da iyalinsancikin nasara.

“Muna duniya dan mu yi iyali, mu yi bauta ga Allah Madaukakin Sarki, mu ci gaba da biyan buƙatunmu na daidaikun jama’a, muyi rayuwa cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, duk da yanayin aikina da iyalina a ko dayaushe suna bayana shi ya sa kuke ganin ‘yan uwa masu zaman lafiya a gaban ku, ina kuma godiya ga ‘yan jarida da kullum suke ba da labarin iyalina daidai, domin ‘yan jarida na iya ginawa da ruguzawa”in ji Yarima Shettima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here