An yi wawason shinkafa lokacin da direban babbar mota ya sare kan mai adaidaita

0
216

An samu tashin hankali a kasuwar Itam da ke ƙaramar hukumar Itu a jihar Akwa Ibom, Bayan kisan da wani direban babbar mota ya yi wa wani mai tuƙa babur ɗin adaidaita.

Wata majiya a kasuwar ta bayyana cewa rikicin ya fara ne a lokacin da direban motar, wanda bahaushe ne, ya ke ƙoƙarin faka motar domin ya sauke buhunan shinkafar cikin sauki duba da yanayin wajen da ya ke a cunkushe da masu adaidaita da tebura da ‘yan kasuwa.

Ana cikin ruɗanin,sai direban ya sauko daga babbar motarsa ​​da adda a hannunsa, inda ya sari kan mai babur ɗin adaidaita, wanda ya mutu sakamakon zubar jini da ya wuce kima.

Wani ganau mai suna Mista Akan Bassey, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar lahadi, kuma ya ɗauki kimanin awa ɗaya kafin ‘yan sanda su isa wurin domin kwantar hankali.

KU KUMA KARANTA:Yadda wata mace ta fille kan jaririnta da adda

Ya ce, “direban babbar motar ya fusata ne saboda yadda masu adaidaita da ‘yan kasuwa suka ƙi ba shi hanya domin ya sami damar faka motar yadda ya kamata a sauke shinkafar.

“Da ya sauko daga motar domin ya nemi wajen ajiye motar, sai suka ƙi, shi kuma kawai ya fito da adda, ana cikin haka sai ya yanke kan mai adaidaita sahun”

Nan take wasu ’yan tada zaune tsaye, suka yi amfani da wannan damar wajen wawashe shinkafar, tare da ƙona motar, yayin da direban motar ya gudu.

An rufe kasuwar saboda afkuwar lamarin, kafin daga bisani a sake buɗe ta, inda ofishin ‘yan sanda na Itam da ke kusa da kasuwar suke jagoranta sintiri a kasuwar.

Shugaban al’ummar Hausawa da Fulani na jihar Akwai Ibom Alhaji Alhassan Sadauki, a lokacin da yake faɗakarwa akan zaman lafiya, ya yi ƙira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen daƙile ruruwar rikicin zuwa na kabilanci.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Odiko Macdon, ya ce rundunar za ta binciki lamarin.

Leave a Reply